Kwanakin baya Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bayyana wani abin da ba a sani ba game da fadar sa da iyalin sa lokacin da yayi wata doguwar hira da Jaridar FT ta Turai.
Sarki Muhammadu Sanusi II wanda yake da ‘Ya ya 12 (mata 7 da maza 5) ya bayyana cewa yana da matan aure 4. Sai dai Amaryar ta sa ba za ta tare ba sai bayan ta kammala Jami’ar a Turai sannan za ta shigo cikin fada.
A tattaunawar da mai martaba yayi, ya bayyana cewa iyalin sa ne su ke dafa masa abincin sa. Bakon da yayi hira da shi ya ga abinci iri-iri wanda su ka hada tuwon shinkafa da waina da dai sauran abubuwan tabawa birjik.
A hirar idan ba ku manta ba Mai martaba Sarkin na Kano ya bayyanawa ‘Dan jaridar cewa daya daga cikin ‘Ya ‘yan sa mata na da burin zama Sarkin Kano nan gaba. Yanzu dai kusan shekaru 3 kenan Sarkin yayi a karaga.
Source :naij hausa
Title :
Abinda Ba'a Sani Game Da Iyalai Naba - Sunusi Lamido Sunusi
Description : Kwanakin baya Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bayyana wani abin da ba a sani ba game da fadar sa da iyalin sa lokacin da yayi...
Rating :
5