Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteres ya yi yabawa kokarin gwamnatin tarayya wajen ceto yan matan makarantar sakandire na Dapchi da yan Boko Haram suka sace a cikin kwanakin nan.
A wata sanarwa da Sakataren ya bayar a birnin New York da ke Amurka, ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta gudanar da bincike kana ta hukunta duk wadanda aka samu da hannu cikin satar yaran kamar yadda NAN ta ruwaito.
Sakataren kuma ya kara jadada cewa ya kamata gwamnatin Najeriya tayi duk mai yiwuwa don ganin cewa an dawo da sauran yaran da ke tsare a tare da yan kungiyar na Boko Haram don mayar da su ga iyalan su.Ya kuma yi kira ga "mahukunta a Najeriya suyi gagawa wajen hukunta wadanda ke da hannu cikin wannan rashin adalcin".
A wata rahoton, jaridar naij ta ruwaito cewa Hukumar sojin Najeriya a ranar Laraba, 21 ga watan Maris ta mika yan mata 106 zuwa ga gwamnatin tarayya.
Guda 104 cikin wadanda aka sako yan makarantar sakandire na Dapchi ne, sai kuma yaro na miji daya da mace daya da yan Boko Haram din suka sako.
Source :naij hausa
Title :
A Hukunta Duk Wanda Aka Kama Da Hanu A Satan Yan Matan Dapchi - MDD
Description : Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteres ya yi yabawa kokarin gwamnatin tarayya wajen ceto yan matan makarantar sakandire ...
Rating :
5