Wasu zakuna biyu da aka yi watsi da su a wasu gidajen namun daji da ke kasashen Syria da Iraki sun koma Afirka Ta Kudu, bayan yaki ya daidaita gidajen adana su da ke kasashen.
A yanzu dai an mayar da zakunan Afirka Ta Kudu ne inda ta zama sabon gidansu.
Kungiyar da ke kula da dabbobi ta Four Paws ta wallafa hotunan zakunan a shafinta na Twitter gabannin kai su Afirka Ta Kudun
A shekarar 2017 ne kungiyar Four Paws ta ceto zakunan daga wasu gidajen ajiye namun daji da ke biranen Mosul da kuma Aleppo.
Mafi yawan namun daji da ke gidan zoo na Mosul sun mutu sakamakon yunwa ko kuma hare-haren bama-baman da ake kaiwa, yayin da aka ceto wasu namun dajin 12 daga gidan zoo na Aleppo.
Sai da aka kai zakunan masu suna Simba da Saeed cibiyar bayar da kulawa ta musamman a kasar Jordan kafin a kai su Afirka Ta Kudun.
Za a kai su sabon matsuguninsu mai girman eka 1,250 da ake ajiye zakuna mai suna Lions Rock, da misalin karfe 1.00 na ranar Litinin a agogon GMT.
Kungiyar da ke kula da dabbobi ta Four Paws ta wallafa hotunan zakunan a shafinta na Twitter gabannin kai su Afirka Ta Kudun
Source :bbc hausa
Title :
Zakunan Syria Da Iraki Sun Gudu
Description : Wasu zakuna biyu da aka yi watsi da su a wasu gidajen namun daji da ke kasashen Syria da Iraki sun koma Afirka Ta Kudu, bayan yaki ya daidai...
Rating :
5