Zakanya ta kashe wata mata a gidan kula da namun dajin birnin Pretoria na kasar Afirka ta Kudu.
Kakakin hukumar Netcare 911, wadda ke bayar da agajin gaggawa Nick Dollman, ya ce hukumarsa ta yi gaggawar kai dauki bayan da aka kira ta gidan namun dajin da ke garin Hammanskraal.
"Abin takaicin shi ne, matar ta samu munanan raunuka kuma nan take ta mutu," in ji Mr Dollman.
Babu cikakken bayani kan abin da ya sa zakanyar ta kai wa matar hari.
Mr Dollman ya ce mutanen da suka je gidan kula da namun dajin ne suka kai wa matar, mai shekara 22, dauki ta hanyar daddanna kirjinta domin numfashinta ya dawo.
Source :bbc hausa
Title :
Zakanya Ta Hallaka Wata Mata A South Africa
Description : Zakanya ta kashe wata mata a gidan kula da namun dajin birnin Pretoria na kasar Afirka ta Kudu. Kakakin hukumar Netcare 911, wadda ke bayar...
Rating :
5