Jam'iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari ya tattara kayansa ya koma garin Dapchi domin ya gano mata 110 da aka yi amannar cewa kungiyar Boko Haram ta sace.
"PDP na son Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da shakatawar da yake yi da jam'iyyar APC a fadar Aso Villa ya nuna yadda ake shugabanci ta hanyar tafiya Dapchi da ke Yobe, domin samun labari da dumi-duminsa kan abin da ya sa aka sace mata 'yan makaranta 110 yana ji yana gani," in ji wata sanarwa da kakakin jam'iyyar Kola Ologbondiyan ya aike wa manema labarai.
Gwamnatin Najeriya ta tura karin dakarun tsaro da jirage domin nemo 'yan matan da aka sace a makon jiya.
Sai dai PDP ta ce abin kunya ne ga shugaban kasar da jam'iyyarsa ta APC su rika biki da shirin zaben 2019 a fadarsa a lokacin da iyayen 'yan matan ke juyayin rashin ganin 'ya'yansu.
Mayakan Boko Haram sun shiga garin Dapchi ranar 19 ga watan Fabrairu, inda suka ya da zango a makarantar 'yan matan, suka yi awon gaba da su.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce satar yaran wani "babban bala'i ne" sannan ya nemi afuwar iyayen matan kan abin da ya faru.
Wannan lamari ya tuna wa duniya sacewar da 'yan Boko Haram suka yi wa 'yan matan makarantar sakandaren Chibok a shekarar 2014.
Iyayen yaran sun nuna matukar rashin jin dadinsu a daidai lokacin da rahotanni ke cewa sojoji sun janye daga wuraren binciken ababen hawa da ke Dapchi wata guda kafin aukuwar lamarin.
Sojojin sun ce sun mika tsaron garin a hannun 'yan sanda, ko da yake rundunar 'yan sandan jihar ta musanta hakan.
An kai hari a Dapchi, wanda ke da nisan kilomita 275k daga Chibok, ranar Litinin din makon jiya, lamarin da ya sa dalibai da malaman Makarantar Koyon Kimiyya da Fahasa ta mata suka ranta a na kare zuwa cikin dazukan da ke kusa
Hakki ne ya kama gwamnatin Buhari — PDP
Dapchi: Shin ba a koyi darasi ba ne daga Chibok?
Mazauna yankin sun ce jami'an tsaron kasar, wadanda jiragen yaki ke rufa wa baya, sun dakile harin.
Da farko dai gwamnatin jihar ta ce babu wanda aka sace, tana mai cewa daliban sun buya ne domin gudun kada maharan su kama su.
Amma daga bisani sun amince cewa an sace mata 110 bayan harin.
Source :bbc hausa
Title :
Yazamo Dole Wa Buhari Ya Tafi Dapchi - PDP
Description : Jam'iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari ya tattara kayansa ya koma garin Dapchi domin ya gano mat...
Rating :
5