A karon farko Saudiyya ta bude cibiyoyin karbar takardun nemai aikin soja ga matan kasar.
An bai wa mata zuwa ranar Alhamis domin su aike da takardun nemai aikinsu a lardunan Riyadh da Makka da al-Qassim da kuma Madina.
Sai dai aikin nasu ba zai ba su damar zuwa fagen daga ba, sai dai kawai ya ba su damar shiga aikin tsaron kasar.
An sanya sharuda 12 ga duk macen da ke son zama soja ta cika su kafin a dauke ta aikin, ciki har da: dole ne ta kasance 'yar kasar, da kuma zama 'yar shekara tsakanin 25 zuwa 35, sannan kuma tana da matakin ilimi na babbar difiloma.
Dole ne matan - da kuma muharramansu - akasarinsu mazajensu, ko iyayensu ko kuma 'ya'yansu maza - su kasance suna zaune a yankin da za a bai wa macen aiki.
Matakin daukar mata a aikin soja na cikin sauye-sauyen da kasar ke gudanarwa a watannin baya-bayan nan domin inganta damar mata a kasar da ake yi mata kallon mai cike da 'tsattsauran ra'ayi.'
A watan Yuni ne Sarki Salman ya amince mata su soma tuka mota, sannan ya amince mata su rika zuwa kallon wasan kwallon kafa.
Saidai masu fafutika suna suka, inda suka ce har yanzu ba a barin mata su yi tafiya ba tare da maza ba.
A karkashin dokar kasar, dole mace ta nemi izini kafin ta yi tafiya ko aure ko kuma gidan yarin.
Source :bbc hausa
Title :
Yanzu Mata Zasu Iya Shiga Aikin Soja-Gwamnatin Saudiyya
Description : A karon farko Saudiyya ta bude cibiyoyin karbar takardun nemai aikin soja ga matan kasar. An bai wa mata zuwa ranar Alhamis domin su aike d...
Rating :
5