Harin makarantar mata a Dapchi a Jihar Yobe yana kara zama kamar na makarantar garin Chibok da mayakan Boko Haram suka abka suka sace dalibai 276 a 2014.
Yayin da ake amai ana lashewa game da batun sace 'yan matan makarantar a Jihar Yobe da ke arewa maso gabacin Najeriya, hakan ya nuna kamar ba a koyi darasi ba ne daga Makarantar garin Chibok da aka sace mata sama da 200 a Jihar Borno.
Batun Dapchi a yanzu yana son ya yi kama da na Chibok.
'Yan kwanaki bayan sace 'yan Matan Chibok, gwamnati ta yi shiru ba ta ce komi, kafin daga baya kuma rundunar sojin Najeirya ta sanar da cewa an ceto dukkanin 'yan Matan kafin ta yi amai ta lashe.
Da farko hukumomin Najeriya ba su yi la'akari da girman al'amarin ba har sai da batun ya ja hankalin duniya bayan kaddamar da kamfen na a dawo da 'yan matan na Chibok wato BringBackOurGirls.
A wannan karon ma an samu rudani, inda aka yi ikirarin ceto 'yan matan, kafin daga baya kuma gwamnati ta fito ta nemi afuwa.
Sannan har yanzu ba a tantance gaskiyar adadin yawan 'yan matan da aka sace ba.
Gwamnatin Yobe ta yi amai ta lashe kan 'yan Matan Dapchi
Wadanne 'kura-kurai' Buhari ya tafka tun hawansa mulki?
Wasu sun ce 'yan mata kimanin 50 ne, yayin da wasu kuma ke cewa 'yan matan sun haura 100.
Kuma har yanzu ba a tabbatar da ko mayakan Boko Haram ne suka yi awon gaba da daliban ba.
Har yanzu akwai ragowar 'yan matan Chibok kusan 100 da ba a gano ba
Iyayen 'yan matan makarantar Dapchi dai sun shiga wani hali da damuwa a yanzu, inda babu wani abu da suke fata illa labarin ceto 'yayansu.
Duk da cewa 'iyayen Dapchi ba za su cire tsammani ba, amma har yanzu akwai iyayen 'yan matan Chibok da ke jiran tsammanin yin tozali da 'yayansu wadanda Boko Hram ta sace yau kusan shekaru 4.
Masharhanta dai na ganin akwai sakaci na hukumomi domin ya kamata ace an dauki darasi daga abin da ya faru a Chibok.
Malam Kabiru Adamu mai sharhi kan al'amuran tsaro a Najeriya, ya ce hakan ya nuna ba wani tanadi ko tsari da aka yi a makarantu domin tsaron dalibai duk da gidauniyar kudi da aka tara domin kare makarantu a taron tattalin arziki na duniya da aka gudanar a Birtaniya.
"Ya dace a dauki matakan tsaro na shiga ta fita a makarantu domin kare sake aukuwar abin da ya faru a Chibok" a cewar Malam Kabiru.
Source :bbc hausa
Title :
Yakamata Akoyi Darasi Daga Chibok-Dapchi
Description : Harin makarantar mata a Dapchi a Jihar Yobe yana kara zama kamar na makarantar garin Chibok da mayakan Boko Haram suka abka suka sace daliba...
Rating :
5