Jam'iyyar Kwaminisanci da ke mulkin China ta gabatar da shawarar cire wata sadara daga kundin tsarin mulkin kasar wacce ta iyakancewa shugaban kasa ya yi wa'adi biyu na shekara biyar-biyar a kan mulki.
Wannan yunkurin zai bai wa Xi Jinping damar ci gaba da zama a matsayin shugaban kasar har bayan lokacin da ya kamata ya sauka.
Ana rade-radin cewa Mr Xi zai nemi tsawaita mulkinsa bayan shekarar 2023.
Babban taron da jam'iyyar ta yi a shekarar da ta gabata ya tabbatar masa da mukamin Shugaba mafi karfin iko a kasar tun bayan mulkin Mao Zedong.
An ci zarafin bakaken fata a bikin sabuwar shekara ta China
An kama yaron da ya yankewa mahaifiyarsa kai a China
Kazalika an sanya manufofinsa a cikin kundin tsarin mulkin jam'iyyar, kuma ba kamar yadda aka saba ba, ba a fadimutumin da zai gaje shi ba
Me aka sani game da wannan yunkuri?
"Kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminisanci ta China ya gabatar da shawarar cire wa'adin shugabanci karo biyu da aka sanya wa shugaban kasa da mataimakinsa a kundin tsarin mulkin kasa," in ji wasu rahotanni.
Babu cikakken bayani kan dalilin bayar da wannan shawara, amma ana sa ran za a yi cikakken bayani nan gaba kadan.
An gabatar da wannan shawarar ce a daidai lokacin da jiga-jigan 'yan kwamitin na tsakiya ke shirin yin taro ranar Litinin a Beijing.
Za a gabatar da shawarar ga 'yan majalisar dokoki, wadanda za su yi taronsu na shekara-shekara ranar biyar ga watan Maris, domin amincewa da ita.
Source :bbc hausa
Title :
Xi Jinping 'zai zama shugaban mutu-ka-raba' a China
Description : Jam'iyyar Kwaminisanci da ke mulkin China ta gabatar da shawarar cire wata sadara daga kundin tsarin mulkin kasar wacce ta iyakancewa sh...
Rating :
5