Majalisar dokokin jihar Zamfara ta kaddamar da bincike kan rahoton wani malami da ya yi wa dalibi duka har ya mutu a makarantar Sankalawa cikin karamar hukumar Bungudu.
A ranar Laraba ne Mataimakin Shugaban Majalisar dokokin Jihar Alhaji Muhammad Abubakar Gummi, ya bayyana wa majalisar faruwar lamarin.
Kuma ya ce sun samu labarin wata daliba da ta samu mummunan rauni a makarantar sakandaren mata ta Kwatarkwashi sakamakon duka da azabtarwa daga mataimakiyar shugabar makarantar.
Hon Abdulmalik Zubairu, dan majalisar da ke wakiltar yankin Bungudu ya ce an kama malamin da ya yi sanadin ajalin dalibinsa mai suna Rayyanu Ahmad.
Wannan na zuwa ne a yayin da a Jihar Imo da ke kudu maso gabashin kasar ma, rahotanni suka ce wata daliba ta mutu a makarantar sojoji ta Obinze, bayan da wasu sojoji biyu suka yi wa dalibar duka saboda ta yi lattin zuwa makaranta.
Rahotannin sun ce sojojin sun sa dalibar mai shekara 15 tsallen kwado har sai da ta kasa tashi, daga baya ne kuma ta rasu bayan an ruga da ita asibiti.
Kisa da dukan dalibai a makarantu ko dai daga malamai da manyan dalibai ba sabon abu ba ne a Najeriya.
An dakatar da 'Principal' saboda zane dalibai a Nigeria
Jigawa: Dalibai 'sun kashe abokinsu don zargin luwadi'
A watan Janairun da ya gabata, hukumomin ilimi a jihar Nasarawa sun dakatar da wani shugaban makarantar GSS Nasarawa Eggon, kan dukan dalibai.
Wani hoton bidiyo da ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda shugaban makarantar ya sa ake yi wa dalibai dukan tsiya.
A cikin hoton bidiyon, an nuna yadda malamin ya daddage yana dukan wasu dalibai da bulala.
A watan Nuwamba ma 'Yan sanda a Kano arewa maso yammacin Najeriya sun taba kama wasu dalibai bakwai a Kwalejin Fasaha ta Ungogo, wadanda aka yi zargi da halaka wani abokin karatunsu da ke ajin karshe.
Haka ma a kwalejin gwamnati da ke karamar hukumar 'Yankwashi a jihar Jigawa, a watan Agustan bara 'yan sanda sun taba kama dalibai 15 da ake zargi da hannu a kisan abokin karatunsu.
An zargi daliban da jefar da gawar dalibin bayan sun kashe shi a ranar 6 ga watan Agusta kan zargin wai dan luwadi ne.
Masharhanta dai na ganin rashin cibiyoyi na jagoranci da bayar da shawara a makarantun sakandare na daya daga cikin abubuwan da ke haifar da wadannan matsalolin.
Sannan da yadda gwamnati ba ta damu da ba bangaren muhimmaci ba a makarantun na sakandare, musamman wajen ilmantar da iyaye da malamai kan muhimmacin ilimin domin halayyar 'yayansu a makarantu.
Wasu na ganin za a iya ladabtar da dalibai ta hanyoyi da dama ba lalle sai an dauki mataki mai tsauri da har zai kai a yi wa dalibai dukan da zai yi sanadin ajalinsu ba.
Source :bbc hausa
Title :
Wani Malami Ya Kashe Dalibinsa Da Bulala A Zamfara
Description : Majalisar dokokin jihar Zamfara ta kaddamar da bincike kan rahoton wani malami da ya yi wa dalibi duka har ya mutu a makarantar Sankalawa ci...
Rating :
5