Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa tace tana tsare da wani jami'in hukumar kwastam wanda ake zargi ya harbe wani mutum a garin Babura da ke cikin jihar Jigawa a arewacin Najeriya.
Wani mazaunin Babura ya shaida wa BBC cewa al'amarin ya faru ne lokacin da mutumin mai suna Alhaji Ummaru da aka harba ke kokarin shiga tsakani, bayan jami'an kwastam sun biyo wani direba, kuma suka cim masa a cikin garin na Babura.
Ya ce sakamakon harbin ne ya sa 'yan uwan mutumin suka yi gayya suka dauke shi kuma kafin su tafi asibiti Allah ya ma shi cikawa.
"Rasuwarsa ce ta hasala mutane suka shiga kona cibiyoyin hukumar kwastam da motocinsu a yankin," a cewarsa.
Sannan ya ce yamutsin ya janyo kona rumfunan kasuwanci da ke kusa da cibiyoyin na kwastom a Babura.
Rundunar 'Yan sandan jihar Jigawa dai ta tabbatar da faruwar al'amarin, kuma kakakinta SP Abdu Jinjiri ya ce suna tsare da jami'in hukumar kwastam wanda ya yi harbin.
Ya kuma ce tuni aka aike da jami'an tsaro domin kwantar da tanzomar.
Source :bbc hausa
Title :
Wani Jami'in Kwastam Ya Harbe Wani A Jigawa
Description : Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa tace tana tsare da wani jami'in hukumar kwastam wanda ake zargi ya harbe wani mutum a garin Babura...
Rating :
5