Rundunar Operation Lafiya Dole, da ke yaki da 'yan Boko Haram, ta ce dakarunta da na Kamaru sun kashe mayakan kungiyar 35.
Sanarwar da mai magana da rundunar Kanar Onyema Nwachukwu ya aike wa manema labarai ta ce lamarin ya faru ne a tsuburan da ke yankin Chadi da kuma yankin Sambisa ranar Litinin.
A cewarsa, dakarun sun far wa yankunan da mayakan Boko Haram ke buya irinsu Kusha-Kucha da Surdewala da Alkanerik da Magdewerne da kuma Mayen, wadanda ke kan iyakar Najeriya da Kamaru, inda suka kashe mayaka 35 sannan suka kwace bindigogi 15 daga wurinsu.
Kanar Nwachukwu ya kara da cewa dakarunsu sun ceto farar hula 603 wadanda Boko Haram ta yi garkuwa da su inda suka kai su Bäma Pulka Towns, kafin a mika su sansanonin 'yan gudun hijira.
"A wani mataki irin wannan, gamayyar dakarun soji sun bi masu tayar da kayar bayan zuwa kauyukan Bokko, Daushe da kuma Gava inda suka kashe biyu daga cikinsu," in ji kakakin rundunar.
Ya ce sun ceto farar hula 194 da aka yi garkuwa da su a kauykan sannan suka rusa gidajen wucin gadin da 'yan Boko Haram suka gina a kauyukan.
"Kazalika, gamayyar dakarun ta kwato kauyukan Miyanti da Wudila, inda suka ceto maza uku, mata 121 da kuma kananan yara 209," a cewar mai magana da yawun rundunar ta Operation Lafiya Dole.
Babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan labari. Sai dai a baya, rundunar ta sha bayar da labarin kashe mayakan Boko Haram tare da ceto mutane da dama.
Source :bbc hausa
Title :
Sojoji Sun Kashe Mayakan Boko Haram 35
Description : Rundunar Operation Lafiya Dole, da ke yaki da 'yan Boko Haram, ta ce dakarunta da na Kamaru sun kashe mayakan kungiyar 35. Sanarwar da ...
Rating :
5