An dauki hoton wani gwoggon biri a kamara wanda irinsa ba su da yawa a duniya, a wani babban gandun daji a Najeriya.
An ga gwoggon birin ne wanda aka fi samu a Najeriya da Kamaru a wurare daban-daban a gandun daji na Gashaka Gumti, kuma ana fatan zai ci gaba da rayuwa.
A karon farko masu kare dabbobi sun ce sun ga wani nau'in dabba jikinsa kamar kunkuru amma mai tsinin baki da ake kira Pangolin a Ingilishi a gandun dajin na Najeriya.
Ana dai danganta gandun dajin a matsayin arzikin kasa, amma namun dajin da ke cikinsa na fuskantar barazana daga mafarauta.
Masu bincike daga gandun dajin Chester, da ke aiki tare da Ofishin kula da gandayen daji a Najeriya, sun yi nazari kan girman gandun namun dajin a Najeriya.
Gandun dajin da aka sani a daji cikin tsaunuka cike da ciyayi na daga cikin gandayen dajin mafi hatsari a yammacin Afirka.
Kamarori sun dauki hotunan dabbobi da ba a taba gani ba a gandun dajin da ma yankin gaba daya, kamar su gwoggon biri
Gandun dajin Gashaka Gumti na cikin gadayen dajin da aka yi watsi da su a Najeriya
Gwaggon Biri na fuskantar barazanar karewa a yankunan Kamaru da Najeriya. Adadin yawansu ya ragu zuwa kasa da 9,000, inda kimanin 1000 ake tunanin suna raye a iyakokin gandun namun dajin.
Gwaggon biri na fuskantar barazana da yawa, da suka hada da farautarsa a matsayin nama da kuma domin magani.
Yanzu masana kare namun daji suna gudanar da bincike a wasu sabbin wurare a gandun domin tantance adadin yawan namun dajin saboda babu wani bincike da aka yi game da yawan dabbobin a tsawo
An ga Pangolin mai tsinin baki a gandun dajin Gashaka Gumti
Kamarori sun dauki hotuna fiye da 50,000 na namun dawar a tsakanin shekara 2015 zuwa karshen 2017.
"Abu ne mai kyau da aka dasa kamarori domin daukar hotuna a gandun dajin wanda aka manta da shi a Najeriya, amma kuma yake dauke da wasu halittu masu muhimmaci a Najeriya da ma Afirka baki daya," a cewar Stuart Nixon.
Masu binciken sun yi mamakin yadda aka samu dabbar Pangolin, wadda yana da wahala a samu nau'in dabbar.
"Babu wanda ya taba ganin babbar Pangolin, babu kuma wanda ya san inda suke," in ji Stuart Nixon. Wannan ne karon farko da aka ga dabbar a Najeriya.
Wannan ya nuna yadda ba kasafai ake samunsu ba da kuma yadda ake shan wahala wajen nemansu da nazari akansu."
Kamarorin da aka dasa sun samo hoton asali na farko kan Damisa, wanda zai iya kasancewa daya daga cikin mafi muhimmaci ga adadin yawansu a yammacin Afirka.
Magen Daji
Sannan an ga Magen daji a cikin hotunan.
"Kamar wannan alama ce da ke nuna tana cikin yawan adadinsu da suka rage a Najeriya," a cewar Stuart Nixon. "Tana da wahalar kamawa, kuma ba a santa ba sosai, kuma babu wani nazari mai zurfi da aka yi game da su."
Gidan Zoo na Chester ya dade yana taimakawa gandun dajin Gashaka Gumti sama da shekaru 20, musamman kokarin baya-bayan nan da suke yi wajen magance barazanar da gandayen daji ke fuskanta.
Ana kare rayukan gandayen dajin amma kuma dabbobin na fuskantar barazana daga mafarauta. Gidan Zoo na Chester ne ke bayar da tallafi ga masu kare gandayen daji da kuma samar da horo na kare gandayen dajin.
Babban Jami'in kula da gandayen daji a Najeriya Yohanna Saidu ya ce yana da wahala a samu wasu gandayen daji da za su fi Gashaka Gumti musamman tsari da kyau.
Source :bbc hausa
Title :
Sirrin Namun Dajin Dake Nijeriya
Description : An dauki hoton wani gwoggon biri a kamara wanda irinsa ba su da yawa a duniya, a wani babban gandun daji a Najeriya. An ga gwoggon birin ne...
Rating :
5