Shugaban Jam’iyyar APC, John Oyegun ya bayyana cewa Allah madaukakin sarki ne ya kawo wa Najeriya Shugaba Muhammadu Buhari don ya mulki Kasar nan.
Oyegun ya fadi haka ne a garin Lokoja da yake karbar wasu ‘yan jam’iyyar PDP da suka canza sheka zuwa jam’iyyar APC.
Oyegun ya kara da cewa jihar Kogi ne za ta fara jan ragamar yi wa Buhari maraba idan har ya amince ya fito takara a 2019. Sannan yayi kira ga mutanen jihar da su maida hankali sannan su ci gaba da mara wa gwamnan jihar su Yahaya Bello baya domin samun nasara ga ayyukan ci gaba da ya sa a gaba.
” Jihar Kogi sun yi sa’ar matashin gwamna mai kwazon gaske. Saboda haka ina kira gareku da ku ci gaba da mara masa baya.” Inji Oyegun.
Dubban ‘yan jam’iyyar PDP ne suka canza sheka a jihar zuwa APC.
Title :
Shugaba Muhammed Buhari zabin Allah Ne – Oyegun
Description : Shugaban Jam’iyyar APC, John Oyegun ya bayyana cewa Allah madaukakin sarki ne ya kawo wa Najeriya Shugaba Muhammadu Buhari don ya mulki K...
Rating :
5