Za a sayar da wasikar da hamshakin dan kasuwar nan da ya kafa kamfanin Steve Jobs ya rubuta domin neman aiki a shekarar 1973 a kan $50,000. (N18m).
Wasikar, wacce Mr Jobs ya rubuta shekara uku kafin ya kafa kamfanin Apple wanda ya sa ya zaman hamshakin attajiri, tana cike da kura-kurai na nahawu da sauran ka'idojin rubutu.
A cikinta, ya bayyana burinsa na kafa kamfanin fasaha, tun ma kafin ya tsunduma cikin harkar.
Ya zayyana manyan abubuwan da ya kware a kansu irinsu "fasahar kere-kere da injiniyancin zane-zane" sanna ya ce "eh" ya fahimci yadda ake sarrafa kwafyuta.
Ba a san wanda Jobs ya aikewa wasikar ba, ko kuma ma ya yi nasara a aikin da yake nema a lokacin.
Ya rubuta cewa sunansa "Steven jobs" sannan adireshinsa shi ne "kwalejin reed", wato makarantar da ya halarta wacce bai dade ba da ke Portland a jihar Oregon kafin ya yi watsi da karatu.
A cikin wasikar, Jobs ya ce ya mallaki lasisin tuki amma da aka tambaye shi ko yana da mota sai ya ce "mai yiwuwa ne, amma watakila ba haka ba ne".
Da aka tambaye shi ko yana da wayar salula, sai ya ce "babu".
A shekarar 2011 ne Jobs ya mutu sakamakon cutar daji yana da shekara 56 a duniya.
Kamfanin gwanjon kayayyaki na RR Auction da ke Boston, Massachusetts ne zai sayar da waskar ta Jobs tsakanin 8-15 Maris.
Source :bbc hausa
Title :
Shin Za ku iya sayen wasika a kan N18m?
Description : Za a sayar da wasikar da hamshakin dan kasuwar nan da ya kafa kamfanin Steve Jobs ya rubuta domin neman aiki a shekarar 1973 a kan $50,000. ...
Rating :
5