A wani faifen bidiyo da BBC ta samu daga hannun wasu dake fafutika tare da sojojin Najeriyar, an ga yadda sojojin ke kaiwa da komowa a wasu sansanoni na wucin gadi a dajin Sambisa.
Sai dai bayan kwana hudu da dakatar da sojojin daga ci gaba da kai farmakin, mayakan Boko Haram cikin motoci dauke da abubuwa masu fashewa sun kai wa sojojin hari.
Shekau ya koma sa kayan mata - Sojoji
Duk inda Shekau yake ku kamo shi nan da kwana 40 - Buratai
An kashe sojojin Nigeria dana Kamaru 7 wasu kuma da dama suka samu raunuka inda kuma aka lalala motocin sojojin da dama.
Sai dai mako guda bayan sojojin sun shiga sansanin da Shekau yake boye sun tarar ya riga ya tsere.
A halin yanzu rundunar sojin Nigeria ta ce za ta bada takuicin dala $8,000 ga duk wanda ya bata bayanai da zasu kaiga kamo jagoran kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau.
Rundunar sojin Nigeria dai ta sha nanata cewa ta cafke ko ta kashe 'yan kungiyar, inda kuma a wani taron manema labaru a Maiduguri, rundunar ta zayyana makaman da ta ce ta kwace daga mayakan Boko Haram.
Source:bbc hausa
Title :
Saura kiris sojojin Nigeria su cafke Shekau suka janye
Description : A wani faifen bidiyo da BBC ta samu daga hannun wasu dake fafutika tare da sojojin Najeriyar, an ga yadda sojojin ke kaiwa da komowa a wasu ...
Rating :
5