Saudiyya ta ce za ta ware kudi $64bn domin bunkasa masana'antunta na nishadantarwa a cikin shekaru goma masu zuwa.
Shugaban hukumar da ke kula da harakokn nishadi a kasar ya ce an tsara shirya abubuwa kimanin 5,000 a bana kawai da suka kunsh har bikin cashewa na Maroon 5 kamar irin wanda ake gudanarwa a Amurka.
Akwai kuma bikin casu na Cirque du Soleil irin wanda ake gudanarwa a kasashen Turai.
Tuni dai Saudiya ta fara aikin gina wajen casu a birnin Riyadh.
Shirin zuba jarin na cikin sabbin manufofin bunkasa tattalin arziki da ake kira Vision 2030 wanda Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya kaddamar shekaru biyu da suka gaba.
Yariman mai shekaru 32 na son karkatar da tattalin arzikin Saudiyya daga dogaro da arzikin fetir, inda aka kara ware kudi a bangaren bunkasa al'adu da nishadi a kasafin kudin kasar.
A watan Disemba ne, gwamnatin Saudiya ta dage haramci kan gidajen sinima.
Kafofin yada labaran Saudiya sun ambato Ahmed bin Aqeel al-Khatib shugaban hukumar harakokin nishadi yana cewa, yana fatar za su dauki mutane 220,000 aiki a bangare nishadi kafin karshen 2018.
'Yan Cirque Eloiz sun yi casu a watan Janairu wanda shi ne karon farko a Saudiyya
"A baya masu zuba jari suna fita saudiya ne su gudanar da ayyukansu, amma a yanzu za a samu sauyi kuma duk wani abu da ya shafi nishadantarwa a nan za a yi shi", a cewarsa.
Mista Aqeel ya ce zuwa 2020 za a ga canji a Saudiya.
Saudiya dai na fatar bunkasa bangaren yawon bude ido domin samun kudaden shiga.
Wadannan dai sabbin abubuwa ne ake gani a kasa irin Saudiya, inda a watan da ya gabata gwamnatin kasar ta sanar da ba mata shiga filayen kwallon kafa domin kallon wasanni da kuma ba mata izinin tukin mota daga watan Yuni.
A bara, Yarima Mohammed bin Salman ya ayyana kudirinsa cewa yana son mayar da Saudiya "matsayin kasa mai sassacin ra'ayin addini tare da bude kofa ga dukkanin addinai da al'adu da mutanen duniya".
Gidan Sarautar Saudiyya, da tsarin tafiyar da lamurran addinin kasar na bin akidar Sunni ne ta Wahabiyanci, inda wasu dokokin musulunci ke da tsauri sosai.
Source :bbc hausa
Title :
Saudiyya zata hanun jarin $64bn a bangaren nishadantarwa
Description : Saudiyya ta ce za ta ware kudi $64bn domin bunkasa masana'antunta na nishadantarwa a cikin shekaru goma masu zuwa. Shugaban hukumar da ...
Rating :
5