Saudiyya ta kori manyan kwamandojin sojinta, ciki har da shugaban ma'aikata, a jerin matakan da masarautar ta dauka da tsakar dare.
Sarki Salman ya maye gurbin manyan hafsoshin sojin kasa da na sama.
Kamfanin dillancin labaran kasar ne ya wallafa jerin sunayen mutanen da aka kora, amma ba a fadi dalilin sallamarsu ba.
Lamarin na faruwa ne a lokacin da yakin da ake yi a Yemen, inda Saudiyya ke jagorantar gamayyar rundunar yaki da masu tayar da kayar baya, ke shiga shekara ta uku.
An yi amannar cewar yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya Mohammed bin Salman, wanda shi ne ministan tsaron kasar, ne ke sa wa ana gudanar da sauye-sauye a kasar.
A bara dai, an daure fitattun 'yan kasar Saudiyya a wani babban otal da ke Riyadh mai suna Ritz-Carlton, ciki har da shugabanni, ministoci da attajirai, a yunkurin da Mohammed bin Salman ke jagoranta na kawar da cin hanci da rashawa.
Source :bbc hausa
Title :
Saudiyya Ta Kori Manyan Hafsoshin Sojan Ta
Description : Saudiyya ta kori manyan kwamandojin sojinta, ciki har da shugaban ma'aikata, a jerin matakan da masarautar ta dauka da tsakar dare. Sar...
Rating :
5