Ana ci gaba da samun rahotannin kan harin da wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai wata makarantar sakandaren 'yan mata da ke garin Dapchi, a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Wani malami na makarantar, wanda mayakan suka nemi ya ba su hanya su shiga ginin makarantar ya shaida wa BBC cewa mayakan sun je neman abinci ne.
Malamin ya ce ya tabbatar mayakan ba su je makarantar don neman dalibai ba sai don satar abinci da kayayyakin bukatu.
Mayakan dai sun yi nasarar tafiya da kayan abinci bayan sun shafe sa'a uku a cikin makarantar.
Babu dai wanda ya ji rauni a harin da aka kai din, kuma tuni aka rufe makarantar tun bayan faruwar lamarin a ranar Litinin.
A yanzu haka dakarun soji ne suke zagaye da makarantar.
Ganau sun ce mayakan sun shiga garin ne suna harbe-harbe da kuma tayar da ababen fashewa da misalin karfe 6 na yamma.
Boko Haram ta kai hari makarantar mata a Yobe
'Yan BH na jin takaicin ana cewa suna lalata da mu - 'Yar Chibok
'Gyaran motar Boko Haram ya sa mun shekara 8 cikin ukuba'
A lokacin da suka isa mashigar makarantar, sai mafi yawan dalibai da malaman suka gudu cikin daji suka buya.
Malamin ya kara da cewa har zuwa lokacin da ake rubuta labarin nan wasu daliban ba su koma ba, amma bai yarda cewa mayakan Boko Haram din ne suka dauke su ba.
Rundunar sojin Najeriya dai na ci gaba da dannawa cikin dajin Sambisa inda nan ce maboyar 'yan Boko Haram, kuma ta ce tana samun nasara sosai.
BBC ta samu labarin cewa saura kiris sojojin Nigeria su kama jagoran kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau a wani farmaki da aka dakatar da su.
Bayan kwana 10 da faruwar hakan kuma sai suka shiga sansani da aka yi amanna can Shekau ke boye, amma sai suka samu ya tsere.
A wani faifen bidiyo da BBC ta samu daga hannun wasu da ke fafutika tare da sojojin Najeriyar, an ga yadda sojojin ke kai wa da komowa a wasu sansanoni na wucin gadi a dajin Sambisa.
Source:bbc hausa
Title :
Satar Abinci Yakai Yan Boko Haram Makaranta A Yobe
Description : Ana ci gaba da samun rahotannin kan harin da wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai wata makarantar sakandaren 'yan mata da k...
Rating :
5