Rahotannin da suka zo wa RARIYA sun nuna cewa mummunan hadarin mota ya rutsa da Daliban Govt Day Misau, inda kimanin dalibai 16 da malamai biyu suka rasu a hanyar Misau zuwa Kano.
Daliban sun yi hadarin ne a hanyar su ta zuwa 'Excursion' a Kano. Dukkan daliban 'yan karamar hukumar Misau ne, inda su kimanin 20 ne sannan, mutum biyu ne kadai suka tsira a hadarin.
Rahotanni sun nuna cewa sabbabin hadarin shine karon da suka yi da tirela a hanya, malaman su biyu sun rasu, yayin da shi ma direban ya rasu.
Source Rariya
Title :
Photos: Hadarin Mota Ya Halaka Dalibai 16 Da Malamai Biyu A Jihar Bauchi
Description : Rahotannin da suka zo wa RARIYA sun nuna cewa mummunan hadarin mota ya rutsa da Daliban Govt Day Misau, inda kimanin dalibai 16 da malamai ...
Rating :
5