Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sanar wa ‘yan Najeriya ko zai tsaya takarar Shugabancin Najeriya a 2019 ko A’a.
Okorocha ya tsokata wa manema labarai haka ne bayan ganawa da gwamnonin jam’iyyar APC suka yi da shugaban kasa a fadar gwamnati.” Dukkan mu gwamnonin jam’iyyar APC muna goyon bayan Shugaba Buhari ya sake tsaya wa takarar shugabancin Najeriya a 2019.
“Bayan tattaunawa da muka yi da shi kan wasu batutuwa da ya shafi kasar nan, mun Kuma mika kokon baran mu gare sa da ya amince ya tsaya takara a 2019.
“Saboda haka kowa ya kwana da shirin cewa lallai kwananan shugaba Buhari zai fito ya bayyana wa ‘yan Najeriya shirin sa. Sai dai muna fata abinda ke zuciyar sa yayi daidai da abin da muke so mu gwamnonin kasar nan.Idan ba a manta ba gwamnonin jam’iyyar APC kaf din su sun bi shugaba Buhari har Daura domin rokon sa ya amince ya fito takara a 2019.
Source :Premium hausa
Title :
Nan Bada Dadewa Ba Buhari Zai Sanar Da Yan Nijeriya Ko Zai Zarce Ko Aa-Rochas
Description : Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sanar wa ‘yan Najeriya ko zai tsaya...
Rating :
5