Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya ce ya yi kura-kurai da yawa a rayuwarsa.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook da Instagram, Zango ya ce amma lokaci bai kure masa na gyara su ba.
Sai dai dan wasan kwaikwayon na Kannywood bai yi cikakken bayani kan abin da yake nufi ba, sai dai a wata hira da BBC a kwanakin baya, ya ce ya yi nadamar fitowa a fina-finai da dama.
Jarumin ya ce wani abu da yake ci masa tuwo a kwarya shi ne yadda wasu 'yan boko suke masa kallon jahili duk kuwa da cewa "na yi karatun bokon sannan kuma ina da ilimin addini."
Source :naij hausa
Title :
Na aikata Kura Kurai Da Dama A Rayuwata-Adam A Zango
Description : Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya ce ya yi kura-kurai da yawa a rayuwarsa. A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook d...
Rating :
5