Hukumomin yaki da shan miyagun kwayoyi da kuma hukumar Kwastam a Najeriya, sun fara aikin dakile shigo da kwayar Tramadol ta barauniyar hanya.
Bincike ya nuna cewa, shan kwayar fiye da kima na sa maye ga bil-adama, inda sakamakon hakan kuma za a iya aikata wasu abubuwa ba tare da sanin an aikata ba.
Likitoci kan bayar da kwayar Tramadol ne domin rage radadin ciwo, amma a yanzu ta na neman zama annoba a tsakanin matasa ko al'ummar da kan sha, ta yadda za suyi aiki fiye da karfinsu, wani sa'ilin ma har ta zamo cuta.
Kazalika likitoci sun ce, shan irin wadannan kwayoyi fiye da kima na iya lalata wasu sassa na jikin dan adam.
Likitoci dai kan umarci a sha kwayar Tramadol ne bisa ka'ida, to amma wasu na wuce gona da iri.
Wani matashi da ke shan kwayar ta Tramadol, ya shaida wa BBC cewa, yana sha ne domin yana jin kasala a wasu lokuta, don haka ya ke sha domin ya ji garau.
Nigeria: NAFDAC ta kama manyan motoci biyu cike da Tramadol
An ki daukar matasa aikin asibiti saboda shan kwaya a Kano
Ana dai yawan amfani da kwayar ne saboda farashinta bai taka kara ya karya ba.
Akasarin direbobin motocin haya da masu dakon kayayyaki na shan wannan kwaya saboda su ji garau.
Bincike ya nuna cewa yadda masu fasa kaurin kwayar suka fahimce karbuwar ta a wajen jama'a, za a iya cewa masu shigo da ita ta barauniyar hanya kasuwarsu ce ta bude.
Source:BBC HAUSA
Title :
Meyasa Ake Shan Kwaya?
Description : Hukumomin yaki da shan miyagun kwayoyi da kuma hukumar Kwastam a Najeriya, sun fara aikin dakile shigo da kwayar Tramadol ta barauniyar hany...
Rating :
5