Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce kamata ya yi 'yan kasar su dora alhakin yin sakaci wajen sace 'yan matan makarantar Dapchi da ke jihar Yobe a kan Shugaba Muhammadu Buhari.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma'a, PDP ta kuma ce ba ma batun sace 'yan matan kawai ba, kamata ya yi 'yan kasar su dora laifin duk wasu abubuwa da mayakan kungiyar Boko Haram ke yi a arewa maso gabashin kasar, kan gwamnatin tarayya.
Sanarwar ta ce: "Gwamnatin Shugaba Buhari ta sa rayuwar 'yan Najeriya cikin hadari ta hanyar yaudarar mutane wajen ba su bayanan karya na cewa sun kawar da masu tayar da kayar bayan, al'amarin da ya sa mutane suka yarda da wannan karya suka kuma daina fargabar cewa akwai abun da ke barazana ga rayuwarsu.
"Idan da a ce gwamnatin APC ba ta yi ta kirkirar karya tana yadawa mutane don samun tagomashin siyasa a 2019 ba, da tuni mutanen wadannan al'ummomi sun dauki matakan kare kansu daga fadawa irin wannan halin."
Sai dai ko a ranar Juma'a fadar shugaban kasar ta fitar da sanarwar cewa ana bai wa batun sace 'yan matan mhimmanci sosai ta ko wanne bangare.
PDP ta kuma kara da cewa gwamnatin ta yi ta kawo rahotanni daban-daban masu rudarwa a kan batun sace 'yan matan, don kawai kokarin boye laifinsu na gazawa wajen kare mutane.
"Abun takaici ne yadda 'yan Najeriya a yau suke fama da gwamnatin da ke cike da farfaganda, take kuma wasa da al'amarin 'yan kasarta.
"A lokacin gwamnatin PDP ba a taba yi wa 'yan Najeriya karya ko boye musu gaskiyar wani al'amari ba. Ana sanya masu ruwa da tsaki a duk wani abu da ya shafe su don kare rayuka da dukiyoyin 'yan kasa."
An samu ceto 'yan matan Chibok da dama a lokacin gwamnatin Shugaba Buhari ta APC
A karshe PDP ta mika sakon jajenta ga iyayen yaran da aka sace tare da addu'ar Allah ya dawo da su lafiya.
Ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro su daina biye wa 'farfagandar APC' su dauki matakan da suka dace don ceto yaran nan.
A ranar Litinin da yamma ne mayakan Boko Haram suka kai hari garin Dapchi inda suka shiga makarntar 'yan mata da ke garin suka sace kayan abinci, malamai da dalibai kuma suka bazama jeji neman wajen buya.
Sai dai bayan kwana biyu da faruwar hakan ba a ji duriyar 'yan mata da dama ba kuma har yanzu babu labarinsu.
Ana yi wa wannan al'amari kallon irin abun da ya faru ga 'yan matan Chibok da Boko Haram ta sace a 2014 a lokacin mulkin jam'iyyar PDP.
A wancan lokacin ma sai da aka shafe tsawon lokacin kafin gwamnatin wancan lokacin ta yi bayani kan ainihin abun da ya faru, har ma aka dinga zarginta da rashin mayar da hankali kan lamarin.
Kuma a lokacin gwamnatin ba ta smau damar ceto ko daya daga cikin fiye da 'yan mata 200 da ak sace ba.
Source :bbc hausa
Title :
Laifin Buhari ne Sace Yan Matan Dapchi-PDP
Description : Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce kamata ya yi 'yan kasar su dora alhakin yin sakaci wajen sace 'yan matan makarant...
Rating :
5