Wani ango tare da kakarsa sun rasa ransu bayan sun bude wani kunshin kyautar auren da aka ba su ya fashe wanda ake kyautata zatan bam ne aka rufe a ciki.
Wannan lamari dai ya faru ne a jihar Odisha da ke gabashin kasar India a ranar Jumma'ar da ta gabata.
'Yan sanda sun ce amaryar ma ta samu munanan raunuka bayan fashewar kunshin kyautar.
Soumya Sekhar da Reema Sahu, sun yi aure ne a ranar 18 ga watan da muke ciki, kuma daga baya ne aka kawo musu kunshin kyautar wanda ke dauke da bam, kuma ba bu suna ko adireshin wanda ya aiko da sakon inji 'yan sanda.
Yadda wani ango ya bata kwalliyar angwancinsa wajen ceto yaro
An kama wani ango saboda gayyatar baƙin bogi a bikinsa
Kafofin yada labarai na kasar sun rawaito cewa, ana bude kunshin kyautar ne sai kawai bam din ya tashi kuma a lokacin akwai amarya da ango da kuma 'yan uwansu da dama a wajen.
Angon tare da kakarsa mai kimanin shekara 85 sun rasu a asibiti, yayin da amarya da wasu mutanen da ke wajen kuma yanzu ke kwance a asibiti suna karbar magani.
'Yan sanda sun ce har yanzu ba a san dalilin da ya sa aka kai wannan kunshin kyauta ba, kuma ba a kai ga gano wanda ya aikata ba.
Source :bbc hausa
Title :
Kyautar Aure Ta Hallaka Ango Da Kakarsa A India
Description : Wani ango tare da kakarsa sun rasa ransu bayan sun bude wani kunshin kyautar auren da aka ba su ya fashe wanda ake kyautata zatan bam ne aka...
Rating :
5