A wata ganawa da manema labarai na jaridar The Cable, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta na iyaka bakin kokarin ta wajen jagorantar kasar nan.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a yayin tofa albarkacin bakin sa bayan da manema labarai suka tuntube sa dangane da yanayin shugabancin jam'iyyar APC.
Sai dai sanatan yana fatan cewa, gwamnatin zata kara hazaka kan hobbasan da ta yi a baya cikin shekarau uku da suka gabata, domin mutanen kirki na kasar nan su dugunzuma wajen kadawa jam'iyyar kuri'un su a zaben 2019.
Kwankwaso yake cewa, wannan shekarar ta karshe da ta yiwa jam'iyyar APC saura tana da matukar muhimmanci.Tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa, har yanzu bai yanke shawarar neman takarar wata kujera a zaben 2019, kuma baya da ra'ayin sauya sheka daga jam'iyyar su ta APC.
Source :naij hausa
Title :
Kwankwaso ya tofa albarkacin bakin sa kan mulkin Buhari
Description : A wata ganawa da manema labarai na jaridar The Cable, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa gwamnatin...
Rating :
5