Daular Borno tsohuwar Daula ce a Afirka da aka kafa tun kafin karni na 10 wacce ta hada da yankunan da yanzu ke cikin Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru da Sudan har Libya.
Daular Kanem ta El Kanemi ta samo asali ne daga daular Saifuwa.
Masana tarihi sun ce mutanen Saifuwa daga Yemen ne suka fara kafa daular musulunci a Borno, tsawon shekaru 1000 da suka gabata.
Muhammad al-Amin ElKanemi ya kafa Daular Kanem ne a karni karni na 18, bayan kawar da daular Saifuwa wadanda sarakunanta suka yi mulki shekaru da dama.
BBC Hausa ta duba tarihin Daular Borno ta hanyar tattaunawa da Masana tarihi Alhaji Zanna Hassan Boguma daraktan da ke kula da al'amuran masarautu a Borno, da Farfesa Adam Muhammad Ajiri na sashen nazarin addinin Islama a Jami'ar Maiduguri, wadanda kuma suka yi kokarin amsa wasu tambayoyi da masu saurare suka aiko.
Asalin kalmar Borno - Tambaya ce da muka samu daga Umar Abubakar da Sani Garba da Ishaq Abubakar Kazaure.
Rubuce-rubucen masana tarihi sun nuna cewa Kalmar Borno ta samo asali ne daga kalmomin Larabci, "Bahar Nur" wato ma'ana kogin haske.
Kuma saboda kasancewar Borno gidan Al Qur'ani gidan Musulunci ne dalilin ke nan da ya sa sarakunan farko suke kiranta "Bahar Nur", ma'ana kogin haske na musulunci.
Amsar tambayoyinku kan masarautar Sarkin Musulmin Nigeria
Mata 100: Kun san macen da ta yi zarra tsakanin mazan Nigeria?
Masanin tarihi Alhaji Zanna Hassan Boguma ya ce Ibn khaldun ya ambaci "Bahar Nur" a rubuce-rubucensa na tarihin musulunci a Afirka.
Daular Borno ta kafu sama da shekaru 1000
Tushen Borno - Wannan Tambaya ce da muka samu daga Umar Musa Dambam daga Bauchi a Najeriya da Buhari Yusuf da Abdulmumin Adamu da Ahmad Adamu Tamadina da Shu'aibu Idris Kofar fada Balangu a jihar Jigawa da Garba Saleh.
Tarihi ya nuna cewa Kanuri da suka kafa Borno daga Yemen suka fito, wato tsatson wani sarki da aka yi a Yemen Said Ibn Dhi Yazan da ake kira Malik al-Himyari tun kafin zamanin Annabi SAW, wanda ya kafa dauloli a India da Fasha.
Tarihi ya nuna mutanen Ibn Dhi Yazan suna cikin wadanda suka amince su ba sahabban Annabi SAW mafaka bayan hijirarsa daga Makkah zuwa Madinah.
Yemen ne asalin Kanurin da suka kafa mulki a Borno daga daular Saifuwa' a cewar Zanna Hassan Boguma.
Shehu Umar Kura Ibn Shehu Muhammad Al-Amin Elkanemi sarki na biyu a Daular Elkanemi
Borno a zamanin Sahabbai - Tambaya ce da muka samu daga Jamilu Bagaraje da Magaji Rabiu da Abubakar Umar Usman da Nasir Abubakar Jaja.
Daular Borno ta yi zamani da Sahabbai, kuma masanin tarihi Alhaji Zanna Hassan Boguma ya ce daular ta kafu ne tun kafin zuwan Annabi SAW.
A cewarsa tarihi ya nuna sarakunan Borno sun aika da wasika suna neman malamai da za su koyar da addini zuwa ga Amr al-As gwamnan Misra, wanda shi kuma ya tura Uqba Ibn Nafi.
"Sarakunan Borno sun karbi malamai daga wajen Ibn Nafi a zamanin Sayyadina Umar RA".
Amma Zanna Hassan Boguma ya ce wasu litattafan tarihi sun nuna cewa a zamanin Sayyadina Usman RA ne.
Sai dai Farfesa Adam Muhammad Ajiri ya ce Gwamnan daular Maghribi a arewacin Afirka Uqba Ibn Nafi yakinsa har ya kawo Borno a shekarar 666, kuma zamanin Khulafa'ur Rashidun ya fara ne daga 632 har zuwa 660.
Ya ce ba za a iya cewa sun yi zamani da sahabbai ba, amma ana ganin watakila a lokacin akwai daular musulunci a Borno, ko da yake an fi tabbatarwa a zamanin Umayyad daga 661 zuwa 750.
"A lokacin akwai binciken da ya nuna daga shekarar 661 zuwa 670 akwai malamai daga daular Umayyad da suka shigo yankin Maghrib har suka iso Borno," in ji Farfesa Ajiri.
Taswirar yankunan Tsohuwar Daular Borno
Saifuwa a Borno da kafuwar ElKanemi - Tambaya ce da muka samu daga Abdurahman Salisu Zaria da Abubakar Goni Kolo da Hassan Yarima K/Huguma da Baba Ali Kabir
Saifawa su ne asalin sarautar Borno, kuma Zanna Boguma ya ce dalilin da ya sa ake kiransu Saifuwa saboda sun fito ne daga Said Ibn Dhi Yazan.
Tarihi ya nuna Saifuwa sun yi sarauta sama da shekara 1000 inda suka yi sarakuna kimanin 113, tun kafin karni na bakwai.
Farfesa Ajiri ya ce bayan Saifuwa sun ci Zaghawa da yaki ne suka kafa daular musulunci a Borno, kuma sun kafa daula ne daga wajajen karni na shida.
Sarakunan farko a daular Saifuwa sun hada da Mai Dugu a shekarar 785 da Mai Fune a shekarar 835 da Mai Aritso a 893, da Mai Katuri a 942 da Mai Ayoma a 961 da Mai Bulu a 1019 da Mai Arki a 1035 da Mai Shu a 1077.
Fadar Shehu Umar Sanda Kyarimi da Majalisarsa a Dikwa
"Tun zamanin Sarkin Saifuwa Mai Hume Djilme a wajajen 1080 aka fara daula ta musulunci har zuwa sauran sarakunan da aka yi", a cewar Zanna Boguma.
Ya ce, a zamanin daular musulunci ta Saifuwa an yi Sarakuna da suka hada da Mai Dunama Humemi da ya yi mulki daga shekarar 1098 zuwa 1150 da Mai Biri Ibn Dunoma da ya yi mulki daga shekarar 1150 zuwa 1176 da Mai Bikoru Ibn Biri Dunomami da ya yi zamani daga 1176 zuwa 1193.
Mai Ahmad ne Sarkin Saifuwa na karshe, kafin zamanin daular ElKanemi.
Farfesa Ajiri ya ce karshen mulkin Saifuwa ya zo karshe ne a lokacin da Fulani suka kawo hari suka ci garin Gazargamu da yaki tsohon babban birnin Daular Borno.
Goni Mukhtar ne ya yaki Gazargamu, inda ya kori Mai na Saifuwa tare da taimakon Shehu El Kanemi.
ElKanemi ne ya taimaka aka kori Fulani daga Borno.
Farfesa Ajiri ya ce bayan an kashe Goni Muktar a Damaturu ne kuma Mai Ahmad na Saifuwa ya rasu, daga nan El Kanemi ya zama Sarki a wajajen 1810 zuwa 1814.
ElKanemi ya ci gaba da mulki a daular Saifuwa duk da cewa shi ba daga zuriyar Saifuwa ba ne.
Farfesa ya ce ElKanemi ya kafa daular ElKanemi 1814 a birnin Kukawa, wato shekaru sama da 200 a yanzu.
1809- Kasuwar Kukawa a tsohuwar Borno
"Idan an hada shekaru kusan 800 na Daular Saifuwa da shekaru sama da 200 zai kasance shekarun daular Borno sama da 1000".
Shehu Mohammed el Amin Elkanemi ya fara kafa daula ne a Ngurno tare da ba Mai Dunoma na Tara Lefami matsayin sarki a Kanem daga daular Saifuwa daga 1814 zuwa 1817.
Mai Ibrahim na hudu Ibn Dunoma Lefami ne ya gaji Dunoma a matsayin Sarkin Saifuwa a Kanem.
Bayan El Kanemi ya karbi mulki ne sarautar Borno ta sauya daga Saifuwa zuwa Shehu ElKanemi.
Masanin tarihi Zanna Boguma ya ce lakabin sarautar Borno ya sauya daga "Mai" ma'ana "Sarki" zuwa "Shehu" bayan kafuwar ElKanemi, sabanin sarakunan farko.
"Bayan ElKanemi ya samu mulkin Borno, daga nan ne ya ce shi ba zai amince a kira shi da "Mai" ba saboda shi malami ne".
"Don haka ya ce zai kira kansa a matsayin Shehu, wato Malami, inda ya hada mulki da malamanta", a cewar Zanna Boguma.
Ya kuma ce: "Wannan ne dalilin da ya sa duk wadanda suka zama sarakuna a Borno ake kiransu Shehu daga gidan El Kanemi."
Shehu Umar Kura ne ya gaji mahaifinsa Shehu Muhammad El Amin ElKanemi a matsayin Sarkin Borno daga 1835 zuwa 1853.
Shehu Abubakar Garbai Ibn Shehu Ibrahim Elkanemi Kakan Shehun Borno na yanzu Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi
Sarakunan El Kanemi - Tambaya ce da muka samu daga Naziri Aliyu Abubakar da Hussaini Aminu da Mohammed Mala Ngarannam da Abdullahi Bala da Shafi'u Idris Umar da muhammad Ali.
Kamar yadda bayanai suka gabata an yi shekaru da dama da kafuwar Daular Borno kafin zuwan ElKanemi. Sarakunan Borno zamanin daular Elkanemi kafin Rabeh ya ci Borno da yaki sun hada da:
Shehu Mohammed Al-Amin Elkanemi 1814- 1846
Shehu Umar Kura Umar (1835 - 1853) Dan Shehu Mohammed Elkanemi
Shehu Abdul Rahman Ibn Muhammad Elkanemi - 1853 - 1854
Shehu Umar Kura Ibn Muhammad Elkanemi- 1854 - 1880
Shehu Bukar Zarami Kura Ibn Umar - 1880 - 1884
Shehu Ibrahim Ibn Umar - 1884 - 1885
Shehu Hashimi Ibn Umar - 1885 - 1893
Shehu Kyari Ibn Bukar Zarami - 1893-1894
Shehu Sanda Limananbe Wuduroma Ibn Bukar Zarami - 1894
Shehu Umar Kura na cikin Sarakunan Borno da suka fi dadewa a mulki.
Sai Shehu Sanda Kyari wanda ya shafe shekara kusan 40 yana mulki.
Shehu Mustapha Umar El Kanemi shi ma sarki ne da ya dade inda ya yi shekara 34 yana mulki.
Shehu Garbai kakan Shehu na yanzu ma ya dade inda ya yi shekara 24 yana mulki.
Daular Borno ta yi zama a karkashin turawan Birtaniya da Jamus
Wanene Rabeh? Tambaya ce da muka samu daga Sani Ali da Nura Bala da ahmad Adam Bagas Minna da Adam Musa Ladan Fulata.
Rabeh Zubair Ibn Fadlallah mutum ne da ya taso daga Sudan, wanda ke sana'ar fataucin bayi, inda yake saye ya kuma sayar da bayi.
Masanin tarihi Zanna Boguma ya ce fataucin bayi ne dalilin da ya sa Rabeh ya yaki Borno .
A 1893 ne Rabeh ya kawo wa Borno hari.
"Rabeh Zubair Ibn Fadlallah ne ya rushe tsohuwar daular Borno bayan ya kaddamar da yaki kuma ya samu galabar kwace iko ya mayar da Dikwa a matsayin babban birnin daularsa".
Rabeh ya kashe sarakunan Borno guda biyu, Shehu Kyarimi da Shehu Sanda Wudoroma.
A 1900 sojojin Faransa na mulkin mallaka suka kashe Rabeh bayan ya yi mulki a shekaru bakwai da watanni bakwai da kwanaki bakwai a Borno.
Bayan sun kashe Rabeh ne suka aza Shehu Sanda Kura daga zuriyar Elkanemi a matsayin Shehun Borno a Dikwa a 1900.
A 1901 suka tube shi suka kuma daura dan uwansa Umar Abubakar Garbai, kakan Shehun Borno na yanzu.
Sarakunan Borno bayan kashe Rabeh
Lokacin Turawan mulkin Mallaka, tsohuwar Masarautar Borno ta rabu gida biyu inda Dikwa ta koma karkashin ikon turawan mulkin mallaka na Jamus, bisa wata yarjejeniya tsakanin turawan Faransa da Birtaniya da kuma Jamus na mulkin mallaka.
Daga baya Abubakar Garbai ya koma Sarkin Borno a yankin da turawan Birtaniya ke iko.
A shekarar 1902 ya fara yin hijira zuwa Monguno kafin daga baya ya koma Maiduguri.
Lokacin da Dikwa ta koma karkashin ikon Birtaniya, an samu Shehu guda biyu, Shehun Borno a Maiduguri da kuma Shehun Dikwa.
Shehu Umar Ibn Abubakar Garbai Elkanemi mahaifin Shehun Borno na yanzu.
Tsarin sarautar Borno. Wannan tambaya ce da muka samu daga Aminudden Ali Dan Hassan.
An kafa masarautar Borno da al'adunta ne a kan tsari na musulunci.
Masanin tarihi Zanna Boguma ya ce a zamanin farko na El Kanemi an bi tsari ne irin na khalifancin Manzo SAW.
Ya ce El Kanemi yana da mashawarta guda hudu wadanda kuma suka kasance kamar majalisar Koli.
"Mutanen sun hada da Malam Muhammed Terab da Malam Ahmad Gonimi da Ibrahim Wadaima da Aji Sudani wadanda suka taimaka masa wajen shinfida tsari na shari'a da adalci a Borno".
Amma ya ce bisa tsari na al'ada Borno tana da tsarin sarautu 3,333, wadanda suka kunshi na 'ya'yan gidan sarki da fadawa da bayi da na Malamai.
Sannan akwai sarautu na sana'o'i kamar na wanzanci da kira da rini.
Amma sarautun da suke da girma da kima sun kai 313.
Source :bbc hausa