Ruwa ne ya ci tauraruwar fina-finan Bollywood Sridevi Kapoor, in ji wani bincike kan gawarta da aka yi a Dubai.
A farko dai an ba da rahoton cewa jarumar, mai shekara 54, ta mutu ne sakamakon bugun zuciya ranar Asabar lokacin da take halartar bikin 'yan uwanta a Dubai.
Wasu majiyoyi sun shaida wa kafafen watsa labarai cewa an gano ta a cikin wurin wankan otal din da suka sauka ba ta motsi.
Sridevi ta shafe sama da shekara 50 tana yin fim, inda ta fito a kusan fina-finai 300. Jaruman Bollywood, da fitattun 'yan kwallon kafa da ,amya 'yan siyasa sun yi matukar kaduwa da jin labarin mutuwarta.
'Yan sandan da ke bincike kan gawa na Dubai ne suka ba da rahoton abin da ya yi ajalin jarumar ga iyalinta da kuma ofishin jakadancin India da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, in ji jaridar the Gulf News.
Jaridar ta kara da cewa fitar da rahoton ka iya jinkirta kai gawar Sridevi gida. An sa ran cewa za a kai gawar tata India ranar Litinin.
Source :bbc hausa
Title :
Kun San Meyayi Ajalin Sridevi Kapoor?
Description : Ruwa ne ya ci tauraruwar fina-finan Bollywood Sridevi Kapoor , in ji wani bincike kan gawarta da aka yi a Dubai. A farko dai an ba da rahot...
Rating :
5