Wata kotun Najeriya ta saki mutum 475 da ake zargi da kasancewa mambobin Boko Haram bayan da aka gano ba su da alaka da kungiyar.
Wata sanarwa da ofishin ministan shari'ar kasar, Abubakar Malami, ya fitar ta ce kotun da ke yin shari'a ga mutanen da ake zargi da shiga Boko Haram wacce ke zamanta a sansanin sojin Kainji na jihar Naija ce ta sallami mutanen ranar Juma'a.
Kakakin ministan, Salihu Othman Isah, ya ce za a kai mutanen wurin gwamnatocin jihohinsu domin a ba su shawarwari da kuma inganta rayuwarsu kafin a mika su ga 'yan uwansu.
A cewarsa, "Cikin mutanen da aka kama har da wata yarinya wacce ke da jaririya 'yar wata uku daga jihar Borno, wacce dan uwanta ya mika ta ga 'yan Boko Haram suka aurar da ita ga abokinsa lokacin tana da shekara 11. An kama ta a 2014 lokacin da take yunkurin tserewa."
Sanarwar ta kara da cewa an kama akasarin mutanen ne saboda zarginsu da kasancewa 'yan Boko Haram ko kuma kin bayar da bayani kan yadda za a kama 'yan kungiyar.
An yanke hukuncin daurin shekara 60 kan kwamandan Boko Haram
Matan Boko Haram na tsaka mai wuya
"Sai dai masu shigar da kara ba su iya tuhumarsu da kowanne laifi ba saboda ba a samu gamsassun shaidu da suka nuna su 'yan Boko Haram ne ba. Don haka ne aka sake su," in ji Salihu Othman Isah
Kafin sakin mutum 475 ranar Juma'a, sai da aka saki mutum 468 da ake zargi da zama mambobin Boko Haram bayan an gano ba su da alaka da kungiyar; sannan an yanke hukuncin daurin daga shekara biyu zuwa 15 ga 'yan kungiyar 45.
A makon jiya kotun ta Najeriya ta yanke hukuncin daurin shekara 60 kan wani dan kungiyar ta Boko Haram.
Mutumin, mai suna Abba Umar, mai shekara 22, wanda kuma kwamanda kungiyar ne ya ce bai yi nadamar zaman dan kungiyar Boko Haram ba.
Wannan ita ce shari'a mafi girma da ake yi wa mutanen da ake zargi da kasancewa mambobin Boko Haram tun lokacin da kungiyar ta soma tayar da kayar baya.
Kotuna hudu ne ke yi wa mutum 1,669 shari'a kan zarge-zargen hannu a rikicin Boko Haram.
Source:BBC HAUSA
Title :
Kotun Nigeria ta saki 'yan 'Boko Haram' 475
Description : Wata kotun Najeriya ta saki mutum 475 da ake zargi da kasancewa mambobin Boko Haram bayan da aka gano ba su da alaka da kungiyar. Wata sana...
Rating :
5