Daya daga cikin jiragen kamfanin Dana a Najeriya ya abka cikin daji a yayin da yake kokarin tsayawa bayan ya sauka a garin Fatakwal.
Jirgin- wanda ya fito daga Abuja ya kamata ya tsaya ne bayan ya sauka, amma rahotanni sun ce sai ya zarce iyakar titin sauka har ya abka cikin daji.
Daga cikin dajin na filin jirgin saman a Fatakwal aka kwashe fasinjojin da ke cikin jirgin.
A sanarwar da ya fitar, kamfanin Dana ya ce ruwan sama da aka tabka ne ya haifar da matsalar da jirgin ya abka daji.
Sanarwar kuma ta ce babu wanda ya ji rauni daga cikin fasinjan jirgin.
Jirgin kamfanin Dana ya taba yin hatsari a Lagos inda mutum sama da 150 suka mutu a shekarar 2012.
Source:bbc hausa
Title :
Jirgin Dana Yafadi A Dajin Fatakwal
Description : Daya daga cikin jiragen kamfanin Dana a Najeriya ya abka cikin daji a yayin da yake kokarin tsayawa bayan ya sauka a garin Fatakwal. Jirgin...
Rating :
5