A daidai lokacin da yan fim suka yi kaurin suna wajen rashin auren junansu dama rashin zaman aure musamman a tsakanin matansu, wadannan jarumai biyu sun kafa tarihi wajen karyata wannan hasashe.
Ma’aurata sannan kuma masu fada aji a masana’antar shirya fina-finan Hausa wato Kannywood, Muhibbat Abdulsalam da angonta babban darakta Hassan Giggs sun nuna irin tarin soyayya da kaunar da suke ma junansu.
A koda yaushe ma’auratan kan yi kokarin nunawa duniya irin kaunar da suke ma junansu wanda hakan ne ya sa suke burge mutane.
Hassan Giggs yana mai godiya da farin ciki samun matar kamar Muhibbat wacce ta kasance tsohuwar jaruma a masana’antar fim.
"Kyuata mafi soyuwa da zaka baiwa yaran ka shine kia so mahaifiyar su. Alhamdulillah da samun wannan kyautar a rayuwa ta" jarumin ya wallafa a shafin sa na Instagram.Shekara goma kenan da auren su wanda Allah ya albarkace su da yara mata su uku Humaira, Azeema da Khadijah.
Source :bbc hausa
Title :
Jaruman Da suka Kafa Tarihi A Kannywood
Description : A daidai lokacin da yan fim suka yi kaurin suna wajen rashin auren junansu dama rashin zaman aure musamman a tsakanin matansu, wadannan jaru...
Rating :
5