Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya bayyana cewa sam sam baya fargabar maka shi a kotu da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi wai don wasu maganganu da ake zargin ya fadi.
A wasikar maida martani da mai taimaka masa kan harkar siyasa ya saka wa hannu ya ci Sanata Sani jarumi ne wanda babu irin kotun da bai shiga ba sannan ba kotu ba har kurkuku yayi balaguro a ciki.Ya ce ko da yake ba a kawo wa sanatan takardar sammaci ba, lauyoyin su a shirye suke da zaran ta iso hannu su fara aiki.
” Duk wanda ba zai Iya jure wa zafi ba, to kada ya yi marmarin shiga dakin girki. Hakan da yayi ba zai sa in dai na fadin gaskiya ba.” Idan baka so a fadi maka gaskiya, sai Ka siya auduga Ka toshe kunnen Ka.
Dole ne duk wanda ya fito yi wa mutane aiki ayi masa zazzaga kowa ya san abin da ake ciki. A haska masa wuta kowa ya gabin da ma aka boye ta bayan hannu.”
Source :premium hausa
Title :
Ina jiran El-Rufai a Kotu – Shehu Sani
Description : Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya bayyana cewa sam sam baya fargabar maka shi a kotu da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Ruf...
Rating :
5