A yayin da gwamnatin Najeriya, ta ce kawo yanzu ta samu adadin 'yan matan da ake zargin kungiyar Boko Haram ta sace a makarantar 'yan mata ta Dapchi da ke jihar Yobe da ya kai 110, jam'iyyar adawa ta PDP a kasar ta ce haki ne ya kama gwamnatin shugaban kasar Muhammadu Buhari.
Cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar, ta yi kira ga gwamnatin shugaba Buharin da kada ta yi wasa da rayukan 'yan kasar.
Sakataren jam'iyyar na kasa, Ibrahim Tsauri, ya shaida wa BBC cewa, a lokacin da aka kama 'yan mata na farko, PDP ke mulki, kuma ba su musanta cewa ba a sace 'yan matan ba, hasali ma sun bi duk matakan kubutar da 'yan matan har suka bar mulki.
Ibrahim ya ce " To yau gashi an sake kwatanta irin abinda ya faru a lokacin gwamnatinmu, kuma a lokacin gwamnatin da ta ce ba bu sauran Boko Haram, to mu abinda muka ce shi ne a gayawa mutane gaskiya".
Sakataren jam'iyyar ta PDP, ya ce ba su gamsu da bayanan da gwamnati ke fada a kan satar 'yan matan ba.
Ibrahim Tsauri, ya ce su sun dauki wannan al'amari da ya faru a Dapchi a matsayin kaddara, amma kuma ga dukkan alamu gwamnatin yanzu ta mayar da shi siyasa, shi yasa ma ba sa daukar shawara kowa sai ta 'yan jam'iyyar su ta APC wadda kuma ta gaza.
PDP ta dora laifin sace 'yan matan Dapchi kan Buhari
Nada matattu a gwamnatin Buhari rashin iya aiki ne - PDP
Gwamnatin Najeriyar dai, ta fitar da wata sanarwa daga ofishin ministan yada labaran kasar, Lai Muhammad, inda ta ce ta samu alkaluman adadin 'yan matan da aka sacen ne bayan tattaunawa da malaman makarantar ta Dapchi da kuma iyayen 'yan matan.
Sanarwar ta kara da cewa, ministan yada labaran kasar, Lai Muhammad, ya ce gwamnati ta dukufa wajen ganin an ceto 'yan matan 110, sannan ta sada su da iyayensu cikin koshin lafiya.
Ya kuma kara da cewa, jami'an tsaro na samun bayanai dangane da inda aka kai 'yan matan kuma tuni sun fara bin sahu.
Za a iya cewa wannan dai shi ne karon farko da gwamnati ta fito ta amsa cewa an sace 'yan matan makarantar ta Dapchi.
Domin da farko dai gwamnatin ba ta amince ba, amma daga bisani ta sanar da cewa an ceto yaran kuma za a sada su da iyayensu.
Sai dai kasa da sa'oi 24, sai labari ya sha bambam cewa yaran nan fa sun yi batan dabo al'amarin da ya dugunzuma iyayensu har ma rahotanni suka ce wasu iyayen sun samu hawan jini sakamakon labarin da ya fito daga bakin gwamnan jihar Yobe .
Source :bbc hausa
Title :
Hakkine Ke Bin Gwamnatin APC-Inji PDP
Description : A yayin da gwamnatin Najeriya, ta ce kawo yanzu ta samu adadin 'yan matan da ake zargin kungiyar Boko Haram ta sace a makarantar 'ya...
Rating :
5