A Najeriya, mahukunta a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin kasar sun ce ba za a bude makarantar sakandiren da aka sace 'yan mata a ciki ba har sai abin da hali ya yi.
A ranar Litinin din data gabata ne aka cika mako guda da sace 'yan matan makarantar ta Dapchi wanda ake zargin wasu mahara sun sace su.
Daya daga cikin 'yan matan sakadiren da ta tsira daga kamun maharan da BBC ta tattauna da ita, ta ce gara ta koma makarantar islamiyya maimakon ta koma makarantar.
Dalibar ta ce, ko da an sanya jami'an tsaro a makarantar tasu, ita kam ta hakura da karatun.
Don haka ko da an bude makarantar tasu ta Dapchi ma, ita kam ta sallama karatu a ciki.
Kimanin 'yan mata 110 gwamnati ta tabbatar da an sace su.
Dapchi: 'Ba mu san halin da 'ya'yanmu ke ciki ba'
PDP ta dora laifin sace 'yan matan Dapchi kan Buhari
An kai hari a Dapchi, wanda ke da nisan kilomita 275k daga Chibok, ranar Litinin din makon jiya, lamarin da ya sa dalibai da malaman Makarantar Koyon Kimiyya da Fahasa ta mata suka ranta a na kare zuwa cikin dazukan da ke kusa.
Iyayen yaran da aka sace sun nuna matukar rashin jin dadinsu a dai-dai lokacin da rahotanni ke cewa sojoji sun janye daga wuraren binciken ababen hawa da ke Dapchi wata guda kafin aukuwar lamarin.
Shugaban Najeriyar, Muhammadu Buhari, ya ce satar yaran wani "babban bala'i ne" sannan ya nemi afuwar iyayen matan kan abin da ya faru.
Kuma gwamnatin Najeriyar, ta ce ta tura karin dakarun tsaro da jiragen yakin domin nemo 'yan mata 110 da aka yi amannar cewa kungiyar Boko Haram ce ta sace su a makon jiya.
Source :bbc hausa
Title :
Gwanda Islamiyya Da Makarantar Dapchi
Description : A Najeriya, mahukunta a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin kasar sun ce ba za a bude makarantar sakandiren da aka sace 'yan mata a cik...
Rating :
5