Gwamnatin Yobe ta yi amai ta lashe kan batun ceto 'yan matan makarantar sakandaren garin Dapchi, inda a yanzu ta shaidawa 'iyayen daliban cewa ba a kubutar da su ba.
Daya daga cikin iyayen 'yan matan ya shaidawa BBC cewa gwamnan Yobe ya same su inda ya shaida masu cewa babu daya daga cikin 'ya'yansu da aka kwato.
Gwamnan ya ce Sojoji har yanzu na ci gaba da farautar mayakan Boko Haram da ake zargi sun yi awon gaba da daliban.
Nan take ne dai wasu daga cikin iyayen suka suma, bayan jin labarin daga gwamna, kamar yadda daya daga cikinsu ya shaidawa BBC.
Wata majiya ta kuma shaida wa BBC cewa an yi ta jifan gwamna Ibrahim Gaidam tare da yi masa ihu bayan da ya shaida musu wannan labari.
A ranar Laraba ne Gwamnatin jihar Yobe ta ce sojojin Najeriya sun ceto 'yan matan makarantar sakandaren garin na Dapchi wadanda mayakan Boko Haram suka yi awon gaba da su, wadanda da fari suka ce ba sace su aka yi ba.
Kuma tun bayan sace su a ranar Litinin bayakan Boko Haram suka kai hari a Makarantarsu ba a sake jin duriyarsu ba.
Amma a ranar Laraba Kakakin gwamnan jihar Yobe Abdullahi Bego ya fitar da sanarwar cewa sojojin Najeriya sun bi 'yan Boko Haram tare da kwato daliban.
Tun da farko dai hukumomi sun ce 'yan matan sun bazama daji ne don neman wajen buya yayin da maharan suka dirarwa makarantar.
Yadda wata 'yar Chibok ta tsere daga hannun Boko Haram
Nigeria:'Yan matan Chibok za su koma wurin iyayensu
'Yan BH na jin takaicin ana cewa suna lalata da mu - 'Yar Chibok
Wani malamin makarantar ma ya shaida wa BBC cewa mayakan ba su kai harin don sace 'yan mata ba sai don 'satar abinci,' kuma sun saci kayan abincin da dama.
Sai dai gwamnatin jihar Yoben ta tabbatar da rashin bayyanar 'yan matan a ranar Laraba da safe, inda ta ce ba a ji duriyarsu ba, sai dai ana ci gaba da neman su a dazuzzukan da ke kusa da garin.
An yi ta samun rahotanni masu karo da juna dangane da batan 'yan matan makarantar sakandaren Dapchi da ke jihar Yobe.
Tun da fari kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato iyayen yaran da jami'an gwamnati na cewa 'yan mata 76 aka ceto, kuma har yanzu akwai 13 da ba a gani ba.
Reuters ya kuma ce an gano 'yan mata biyu da suka mutu, amma ba a bayyana abun da ya yi sanadin kashe su ba.
A ranar Litinin ne mayakan kungiyar Boko Haram suka kai hari makarantar inda suka yi ta harbe-harbe tare da tayar da abun fashewa.
Rahotanni sun ce maharan sun sace kayayyaki daga makarantar bayan sun tarar wasu daliban da malaman sun tsere.
Source :bbc hausa
Title :
Gwamnatin Yobe ta yi amai ta lashe Abinta
Description : Gwamnatin Yobe ta yi amai ta lashe kan batun ceto 'yan matan makarantar sakandaren garin Dapchi, inda a yanzu ta shaidawa 'iyayen da...
Rating :
5