Gwamnatin Najeriya ta tuhumi shugaban riko na hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati, EFFC, Ibrahim Magu da babban lauyan kasar Mr. Festus Keyamo.
An tuhumi mutanen biyu ne saboda tuhuma kan cin hanci da suke yi wa shugaban kotun kula da da'ar ma'aikata, Mr. Danladi Yakubu Umar.
Kafar watsa labarai ta The PRNigeria ta ce ta samu wasika biyu na tuhuma da aka aike wa Magu and Keyamo.
A cikin wasikun, wadanda aka aike musu ranar 16 ga watan Fabrairu na shekarar 2018, an bukaci Ibrahim Magu ya aika da amsarsa ga ministan shari'a kafin ranar Talata, 20 ga watan Fabrairu.
'Yan bindiga sun kai hari gidan shugaban EFCC Ibrahim Magu
Shin Buhari zai cire Ibrahim Magu?
Wasikar ta nemi shugaban na EFCC ya yi bayani kan dalilan da suka sanya shi ya tuhumi shugaban kotun kula da da'ar ma'aikata da laifin cin hanci da rashawa duk da yake sau biyu EFCC na wanke shi daga zarge-zargen cin hanci.
Kazalika, wasikar da aka aike wa Mr. Festus Keyamo SAN, wanda ake zargi da zama lauyan Ibrahim Magu, ta nemi ya yi mata bayani kan wanda ya sa shi ya shigar da kara kan Danladi Umar.
Ana zargin shugaban kotun kula da da'ar ma'aikatan ne da laifin cin hanci na N10m, ko da yake sau biyu ana wanke shi a shekarar 2015 da kuma 2016, a cewar The PRNigeria.
BBC ta yi kokarin jin ta bakin Ibrahim Magu ta hanyar mai magana da yawun hukumar EFCC din Wilson Uwajeren, amma har zuwa lokacin rubuta wannan labari wayarsa a kashe take.
Source:bbc hausa
Title :
Gwamnatin Nigeria 'ta tuhumi' Shugaban EFCC Ibrahim Magu
Description : Gwamnatin Najeriya ta tuhumi shugaban riko na hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati, EFFC, Ibrahim Magu da b...
Rating :
5