Gwamnatin jihar Yobe ta nemi afuwa kan labarin ceto 'yan matan makarantar sakandaren Dapchi da mayakan Boko Haram suka abka makarantarsu suka yi awon gaba da su.
A sanarwar afuwa da Abdullhi Bego kakakin gwamnan jihar Yobe ya rabawa manema labarai ciki har da BBC, ya ce sun bayar da sanarwar ceto 'yan matan ne bisa bayanin da suka samu daga daya daga cikin hukumomin tsaro da ke yaki da Boko Haram.
Kuma ya ce sun fadi an ceto 'yan matan ne, domin ba su da wani shakku a kan labarin da suka samu daga hukumar tsaron.
"Yanzu mun fahimci cewa labarin da muka dogara da shi da har ya sa muka fitar da sanarwa ba gaskiya ba ne, gwamnatin Yobe na neman Afuwa", a cewar sanarwar da ke dauke da sa hannun Abdullahi Bego, kakakin gwamnan Jihar Yobe.
Sannan sanarwar ta tabbatar da cewa gwamnan jihar Yobe Ibrahim Gaidam ya gana da iyayen 'yan matan da aka sace a garin Dapchi, kamar yadda wasu daga cikin iyayen suka shaidawa BBC tun da farko.
Gwamnatin Yobe ta yi amai ta lashe kan 'yan Matan Dapchi
'Yan BH na jin takaicin ana cewa suna lalata da mu - 'Yar Chibok
Gwamnan ya bukaci ma'aikatar ilimi da hukumomin makarantar su hada hannu da jami'an tsaro domin tabbatar da adadin yawan 'yan matan da aka sace tare da tuntubar iyayensu domin samun wasu bayanan da za su taimaka wa binciken da ake yi domin gano su.
Tun da farko ne daya daga cikin iyayen 'yan matan ya shaidawa BBC cewa gwamnan Yobe ya same su inda ya shaida masu cewa babu daya daga cikin 'ya'yansu da aka kwato.
Kuma nan take ne wasu daga cikin iyayen suka suma, bayan jin labarin daga gwamna.
Wata majiya ta kuma shaida wa BBC cewa an yi ta jifan gwamna Ibrahim Gaidam tare da yi masa ihu bayan da ya shaida musu wannan labari.
A ranar Laraba ne Gwamnatin jihar Yobe ta ce sojojin Najeriya sun ceto 'yan matan makarantar sakandaren garin na Dapchi wadanda mayakan Boko Haram suka yi awon gaba da su, bayan da fari sun ce ba sace su aka yi ba.
A sanarwar da Kakakin gwamnan jihar Yobe Abdullahi Bego ya fitar ya ce sojojin Najeriya sun bi 'yan Boko Haram tare da kwato daliban sama da 50.
Source :bbc hausa
Title :
Gwamnan Jihar Yobe Yanemi Afuwa Agun Mutanen Dapchi
Description : Gwamnatin jihar Yobe ta nemi afuwa kan labarin ceto 'yan matan makarantar sakandaren Dapchi da mayakan Boko Haram suka abka makarantarsu...
Rating :
5