Wasu fulani makiyaya a Najeriya, na korafin cewa babu wani abin kirkin da suke mora daga mulkin demokuradiyya a kasar, sai ma zargin da suke yi cewa ana kwace musu abin da suka gada tun zamanin Turawan mulkin mallaka, irin su burtali da filayen kiwo.
Wannan ta sa wasu kungiyoyin makiyaya da ke jihar Jigawa suka fara wani gangamin wayar da kan mutanensu a kan muhimmancin mallakar katin zabe da nufin amfani da shi wajen zabar shugabannin da za su kare muradansu a nan gaba.
Alhaji Ya'u Haruna Malam madori na daga cikin wadanda suka jagoranci gangamin, ya kuma shaidawa BBC cewa sun gaji da turawa 'yan siyasa mota amma su na bada musu kura.
Dan haka yanzu sun umarci duk wanda shekarunsa suka kai yin zabe, mata da maza, har da tsaffi su je dan yin rijistar mallakar katin yin zabe.
Ya ce a yanzu ta kai kawai su ke yi, babau ruwansu da kabilar da mutum ya fito. Fatansu kawai wanda zai kare muradunsu da ciyar da al'umar fulani makiyaya gaba dan su ma su dandani romon dimukradiyya.
Fulanin dai na kokawa kan yadda idan asara ta afka musu ba bu wanda ya ke musu jaje bare kuma tallafi, amma da zarar ambaliyar ruwa ta afkawa takwarorinsu manoma ba a daukar lokaci ake tara musu tallafi ta kowacce fuska.
Dan haka su ma a yanzu, za su bude ido dan zaben shugaban da zai tabbatar da mafarkinsu na samun ingantacciyar rayuwa.
Source :bbc hausa
Title :
Damu za'ayi Zabe Mai Zuwa-Makiyaya
Description : Wasu fulani makiyaya a Najeriya, na korafin cewa babu wani abin kirkin da suke mora daga mulkin demokuradiyya a kasar, sai ma zargin da suke...
Rating :
5