Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da yan majalisar kasa matsayar sa kan kudirin kafa Hukumar Zaman Lafiya na Peace Corp a cikin wata wasika da ya aike kuma Kakakin Majallisar na Wakilai Dogara Yakubu ya karanta a gabar majalisar ranar Talata.
Shugaba Buhari ya bayyana matsalolin rashin tsaro da rashin isashen kudi da gwamnatin tarayya ke fama da su a halin yanzu a matsayin dalilan da ya sa ba zai iya amince wa da kudirin na kafa Hukumar Zaman Lafiyar ba.
Buhari ya kuma kara da cewa duk ayyukan da hukumar za tayi akwai hukumomin tsaro da ke gudanar da su a yanzu saboda hakan ya ce maimaici ne kawai.
Majalisar Tarayyah ta karanto kudirin kafa dokar ta Peace Corps ne tun a shekarar 2017 bayan an dauki lokaci mai tsawo ana dauki ba dadi tsakanin Jami'an Hukumar da sauran hukumomin tsaro na Najeriya.
Galibin yan Najeriya musamman matasa dai sun rai cewa shugaban kasan zai amince da kudirin don suna ganin kafa hukumar zai rage radadin talauci da suke fama dashi ta hanyar samar da aikin yi.
Source :naij hausa
Title :
Dalilin Dayasa Ban Sa Hanu Akan Takardar peace Corp Ba-Buhari
Description : Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da yan majalisar kasa matsayar sa kan kudirin kafa Hukumar Zaman Lafiya na Peace Corp a cikin wata wasika ...
Rating :
5