Sai dai Malam Bashir ya ce labarin ba shi da kanshin gaskiya, yana mai cewa "ko jiya [Talata] na yi magana da 'yar uwarsa da ke jinyarsa a asibitin Jamus kuma ta shaida min cewa yana samun sauki sosai."
Sai dai tun bayan da aka tafi da shi Jamus ba a sake jin wani abu na labarin halin da yake ciki ba daga bakunan wadanda ke da kusanci da fadar shugaban, ko da kuwa a kafafen sada zumunta ne.
An sallami Yusuf Buhari daga asibiti a Abuja
Dan Shugaba Buhari ya karye a sanadiyyar hatsarin babur
Kakakin na shugaban kasa bai fadi ranar da Yusuf Buhari zai koma Najeriya ba.
A farkon watan Janairu ne aka sallami dan Shugaban kasar daga wani asibitin Abuja bayan hadarin da ya yi a watan Disamba.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin watsa labarai Garba Shehu ya fitar, ta ce lamarin ya faru ne a unguwar Gwarimpa da ke birnin da daren ranar Kirstimeti.
A cewar Garba Shehu, "Ya karye a kafa sannan ya ji rauni a kansa sakamakon hatsarin. Kazalika an yi masa tiyata a wani asibiti da ke Abuja amma yanzu yana samun sauki".
'Ya'yan masu hannu da shuni kan yi wasan tseren babura akai-akai a wani yanki na kwaryar birnin Abuja, lamarin da ake gani na cike da hatsari.
A shekarun baya, hukumar birnin tarayyar ta haramta yin irin wannan tsere bayan wasu rahotanni da aka samu na tukin ganganci da masu tseren ke yi.
Source:bbc hausa
Title :
Dagaske Ne Dan Shugaban Kasa Buhari Ya Rasu?
Description : Sai dai Malam Bashir ya ce labarin ba shi da kanshin gaskiya, yana mai cewa "ko jiya [Talata] na yi magana da 'yar uwarsa da ke ji...
Rating :
5