A kalla mutane 17 aka tabbatar da mutuwarsu, ciki har da kananan yara a birnin Maputo, wasu da dama kuma suka ji mummunan rauni a lokacin da bola ta rufto kansu.
Jami'ai a yankin sun ce wata bola da ta yi torokon mita 15 ita ce ta rufto, a lokacin da ake tafka ruwan sama da tsakar ranar Talata.
Wurin da bolar ta ke dai, matsugunin daruruwan matalauta da suka gina dakunansu da langa-langa ko katako ne.
Bolar ta bi ta kan wasu gidaje biyar da ke gefenta.
Ma'aikatan ceto na ci gaba da tona bolar ko za su sake samun wasu mutane ko kayan da lamarin ya rutsa da su.
Mai magana da yawun hukumar agajin gaggawa, Leonilde Pelembe, ya yi gargadin a yi taka tsantsan don ta yiwu akwai karin mutanen da bolar ta danne.
''Bayanan da muka samu daga hukumomin yankin sun ce mutanen da suke zaune a wurin bolar sun fi wadanda aka ba mu bayanin sun mutu, '' in ji Mista Pelembe.
Gundumar Hulene da ke Maputo, daya ne daga cikin wuraren da ba a damu da su ba a birnin. Yawancin mazauna gundumar su na samawa kansu matsuguni ne ko dai a can saman bolar ko kuma a gefe, ciki kuwa har da kananan yara.
Bolar ba wai ta na zame musu hanyar samun abinci ba ne kadai, har ta kan zama sanadin samun kudaden shiga kamar yadda wakilin BBC Jose Tembe ya bayyana.
Source :bbc hausa
Title :
Bola Ta Hallaka Yara 17 A Mozambique
Description : A kalla mutane 17 aka tabbatar da mutuwarsu, ciki har da kananan yara a birnin Maputo, wasu da dama kuma suka ji mummunan rauni a lokacin da...
Rating :
5