Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari wata makarantar mata na kwana da ke garin Dapchi a jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya.
Shaidu sun ce wani ayarin mayakan cikin motocin akori kura ne su ka isa makarantar inda suka yi ta harbe-harbe kuma tare da tayar da abun fashewa.
Sai dai 'daliban da malaman makarantar sun tsere ne bayan da hayaniyar ta basu alamar cewa wani abu na faruwa a cikin gari.
Yadda wata 'yar Chibok ta tsere daga hannun Boko Haram
Nigeria:'Yan matan Chibok za su koma wurin iyayensu
Rahotanni sun ce maharan sun sace kayayyaki daga makarantar bayan sun tarar daliban da malaman su tsere.
Kawo yanzu dai an kai karin jami'an tsaro zuwa garin.
A shekarar 2016 ne dai wani bincike ya gano cewa har yanzu babu cikakken tsaro a makarantu a wasu jihohi dake arewa maso gabashin Najeriyar.
Binciken wanda cibiyar bunkasa rayuwar mata, Women Advocate Research and Documentation Centre, da kuma Gender Equality, Peace and Development Centre suka gudanar, ya nuna babu ingantaccen tsaro na koyon karatu a makarantun gwamnati musamman a jihar Borno.
Source:bbc hausa
Title :
Boko Haram ta kai hari makarantar mata a Yobe
Description : Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari wata makarantar mata na kwana da ke garin Dapchi a j...
Rating :
5