Bangaren tattalafawa kafafen watsa labarai na duniya na BBC, wato BBC Media Action ya ce ya kori ma'aikatansa shida saboda samunsu da laifin kallon fina-finan batsa a kwamfutocin wurin aikinsu.
Ya ce lamarin ya faru ne a ofisoshinsa da ke kasashen waje a cikin shekara goma da suka wuce kuma dukkan mutanen da aka kora 'yan kasashen waje ne.
BBC Media Action ya samu tallafi na kimanin fam miliyan 70 daga hukumar ci gaban kasashe ta Burtaniya cikin shekara biyar da suka wuce.
Ya ce ba shi da wata shaida da ke nuna cewa ma'aikatan sun ci zarafin wani ko wata.
Wannan lamari na faruwa ne a daidai lokacin da aka kara sanya ido sosai kan BBC Media Action, bayan zargin lalata da aka yi wa ma'aikatan kungiyar ba da agaji ta Oxfam a Haiti.
Hukumar ci gaban kasashe ta Burtaniya ta bukaci dukkan kungiyoyin bayar da tallafin kasar da ke aiki a kasashen waje su bayar da tabbacin cewa za su kare mutunci da ka'idojin aiki.
BBC Media Action ya ce ya bayar da wannan tabbacin.
"Mun yi nazari kan abubuwan da suka faru a shekara 10 game da cin zarafi. An gano cewa ma'aikata shida sun kalli batsa kuma an gudanar da bincike," in ji sanarwar da BBC Media Action ya fitar.
Ya kara da cewa zai ci gaba da kare dokokin da suka shafi ayyukan da yake yi.
Source :bbc hausa
Title :
BBC Takori Ma aikatan Ta Sabida Kallon Batsa
Description : Bangaren tattalafawa kafafen watsa labarai na duniya na BBC, wato BBC Media Action ya ce ya kori ma'aikatansa shida saboda samunsu da la...
Rating :
5