Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana zargin sa ce 'yan matan sakandiren Dapchi da aka yi a kwanakin baya-bayan nan a matsayin wani bala'i da ya shafi kasa baki daya.
A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar, shugaba Buharin, ya ce gwamnatinsa za ta tura da karin sojoji da kuma jiragen saman yaki zuwa yankin domin kubatar da su.
Sanarwar ta fito ne bayan kwana hudu da aka sace wasu dalibai mata da ke karatu a wata sakandiren gwamnati da ke jihar Yobe.
Har yanzu dai ba san iya adadin 'yan matan da suka bace ba, amma kuma wasu iyayen yaran sun shaidawa BBC cewa, 'yan matan da aka sacen sun fi 100.
Shugaban Najeriyar, ya ce sojoji na nan na neman 'yan matan sakandiren.
Ya ce jiragen saman yaki na ta shawagi a yankin ba dare ba rana.
Kimanin kwanaki hudu ke nan tun bayan da wasu masu tayar da kayar baya suka kai hari makarantar, kuma har yanzu ba bu wani cikakken bayani daga gwamnati a kan adadin daliban da maharan suka yi awon gaba da su.
Iyayen yaran sun kasance cikin bacin rai da damuwa.
PDP ta dora laifin sace 'yan matan Dapchi kan Buhari
Nigeria; Sojoji sun ceto 'yan matan makarantar Dapchi
Kwanaki biyu tun bayan sace 'yan matan, mahukuntan jihar ba su yarda da cewa an sace su ba.
A ranar Larabar data gabata ne, gwamnatin jihar ta Yobe ta ce an kubutar da wasu daga cikinsu, amma kuma ba gaskiya ba ne.
Iyayen yaran wadanda suke a fusace sun jefi ayarin motocin gwamnan jihar da duwatsu bayan da suka samu wannan labari.
Yayin da a jiya Jumma'a kuma daya daga cikin iyayen 'yan matan ya shaida wa BBC cewa, yana boye a wani waje saboda 'yan sanda na nemansa ruwa a jallo saboda jifan da aka yi.
Tuni dai aka kama mutum uku sakamakon jifan ayarin motocin gwamnan ciki har da mahaifin daya daga cikin 'yan matan.
Wasu 'yan Najeriya na kallon lamarin da kamar yadda ya faru a shekarar 2014 inda aka sace 'yan matan sakadiren Chibok, da gwamnati ba ta amince da an sace 'yan matan sakandiren ba.
Source :bbc hausa
Title :
Bala'in Daya Shafi Kasane Sace Yan Matan Dapchi-Buhari
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana zargin sa ce 'yan matan sakandiren Dapchi da aka yi a kwanakin baya-bayan nan a matsayin ...
Rating :
5