Sabon rahoton kungiyar Transperancy International da ke yaki da cin hanci da rashawa a duniya ya ce, har yanzu babu wani sauyi da aka samu a Najeriya a kan yaki da matsalar.
A rahoton da kungiyar ta fitar ta ce Najeriya ce kasa ta 148 daga cikin jerin kasashe 180 da kungiyar ta yi nazarin girman matsalar a 2017.
Transparency ta ce Najeriya ta samu maki 27 ne kacal daga cikin maki 100 da ya kamata ace kasa ta tsira daga matsalar rashawa.
Rahoton kungiyar ya ce matsalar ta kara tsanancewa a Najeriya ne idan aka kwatanta da alkalumman shekarar 2016 inda kasar ta samu maki 28. kuma a matsayin kasa ta 136 a duniya.
Daga matsayi na 136 a 2016 a bana Najeriya ta koma ta 148 a cewar rahoton.
Rahoton kuma ya ce a Nahiyar Afrika Najeriya ce ta 32 daga jerin kasashe 52 da Transperency ta yi nazari kan girman matsalar rashawa.
A cewar rahoton na 2017, Najeriya ce ta biyu a kasashen da matsalar ta fi yin kamari a Afirka bayan Botswana.
Kungiyar CISLAC reshen kungiyar Transparency International da ke yaki da rashawa a Najeriya ta ce sakamakon rahoton abin damuwa ne.
A wata sanarwar bayan fitar da rahoton, CISLAC ta ce tun hawan gwamnati mai ci a yanzu da ke da'awar yaki da cin hanci da rashawa, babu wani hukunci da aka yanke kan 'yan siyasar da aka samu da laifin rashawa.
CISLAC ta ce wannan koma-baya ne a yaki da cin hanci da rashawa, kuma hakan ya tabbatar da girman cin hanci da rashawa musamman rashawa a siyasa da alfarma da azurta dangi.
Kungiyar ta ce duk da akwai dubarun yaki da rashawa gwamnati mai ci ta tsara a 2017 da wasu kudururruka da ta yi alkawali a cikin gida da kasashen waje amma har yanzu ba wani abin azo gani da aka aiwatar.
Nigeria: Kun taba jin maciji ya hadiye naira miliyan 36?
'Abin da ya sa aka zabi Buhari jagoran yaki da rashawa na Afirka'
Gwamnatin Nigeria 'ta tuhumi' Shugaban EFCC Ibrahim Magu
A cikin sanarwar, CISLAC ta bayar da wasu shawarwari da ta ke ganin idan an bi za a iya shawo kan girman matsalar rashawa a Najeriya.
Shawarwarin sun hada da fadada dubarun yaki da cin hanci da rashawa zuwa karkara tare da hada hannu da kungiyoyin fararen hula domin su sa ido tare da aiwatarwa.
Da kafa kotuna na musamman kan yaki da rashawa tare da nada alkalan da aka tabbatar tsabtatattu ne.
Sannan da karfafawa hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa da kariya ga masu kwarmato da kuma karfafawa kafofin watsa labaru.
'Yan Najeriya sun zabi Buhari don yaki da rashawa
Tun a hawansa kan mulki, shugaba Buhari ya bayyana cewa cin hanci da karbar rashawa ba su da wuri a gwamnatinsa, abin da ya sa wasu ke tunanin zai yi irin ba-sani ba-sabon da ya yi a lokacin yana mulkin soja a shekarar 1984.
Gwamnatin Buhari ta kwato kudade da wasu jami'an gwamnatin da suka gabata suka kwace, sai dai har yanzu babu wanda aka gurfanar a kotu.
Sannan gwamnatin Buhari ta sha musanta zargin cewa ta fi karkatar da yaki da cin hanci da rashawa ga 'yan adawa, maimakon yakar matsalar da shugaban ya ce ita ce ta hana kasar ci gaba.
A watan Oktoban 2017 ne Buhari ya kori sakataren Gwamnatinsa Babachir Lawal, da kuma shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA Ambasada Ayo Oke da aka samu da almundahana.
Source :bbc hausa
Title :
Ba Sauyi Haryanzu Akan Rashawa A Nijeriya-Kungiyar Transperancy
Description : Sabon rahoton kungiyar Transperancy International da ke yaki da cin hanci da rashawa a duniya ya ce, har yanzu babu wani sauyi da aka samu a...
Rating :
5