Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma a majalisar dattawan Najeriya, Dino Melaye, ya caccaki jami’yyarsa na APC da rashin cika alkawuran da akayiwa yan Najeriya.
Sanata Dino Melaye ya fito karara ya soki jam'iyyarsa na APC kan mawuyacin halin da yan Najeriya ke ciki.
“Gwamnatin APC ta zama hukumar koke-koke. Ina fadan wannan ba tare da tsoro ba. Koke-koke sun fi yawa a APC da fadar shugaban kasa fiye da ayyukan da akayi.
Ba zai yiwu mu cigaba da haka ba. Shugaban kasa ya fadi kwanaki biyu da suka gabata ya ce mu zanna lafiya amma ina mai cewa, ba zai yiwu a zauna lafiya ba cikin zalunci.Al’umma na cikin yunwa, akwai talauci ko ina, kuma ga rashin aikin yi da yayi yawa. Ba’a yanke shawari ba, kuma ana saon zaman lafiya. Babban hakkin gwamnati shine tsaron jama’a da jin dadinsu. Babu tsaro kuma babu jin dadi,”. YaceYa kara da cewa Najeriya na cikin mawuyacin halin rashin lafiya.
Wajibi ne a kawo gyara. Yin shiru zalunci ne idan abubuwan da bai dace ba na faruwa.
Zaku tuna cewa mutane sun caccaki sanata Dino Melaye akan yin alfaharin ginawa al’ummarsa wani kwalbati da sunan gada. Jama’an sun ce yan siyasanmu sun rainawa jama’ansu hankali idan har ana alfahari da abubuwa irin wannan.
Source :naij hausa
Title :
APC Sun Kunyata Yan Nijeriya - Dino Melaye
Description : Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma a majalisar dattawan Najeriya, Dino Melaye, ya caccaki jami’yyarsa na APC da rashin cika alkawuran...
Rating :
5