Babban mai baiwa shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari shawara kan harkokin tsaron kasa Manjo Janar Babagana Munguno (Mai Ritaya) a jiya Talata ya bayyana cewa rundunar sojin saman kasar nan ta ware akalla jiragen yaki 100 domin su je neman 'yan matan makarantar Dapchi.
Manjo Janar Munguno dai ya ayyana hakan ne lokacin da yakai wa gwamnan jihar ta Yobe inda lamarin ya auku ziyarar bangirma a ofishin sa inda ya kuma jaddada masa cewa jami'an tsaron Najeriya za su gano 'yan matan.
A baya dai mun samu cewa Kawo yanzu dai labaran da muke samu daga majiyoyin mu na nuni ne da cewa jami'an rundunar sojin Najeriya sun dora alhakin sace 'yan matan Dapchi da aka yi a cikin satin da ya gabata a dalilin sakacin 'yan sandan Najeriya.
Mai magana da yawun rundunar ta sojoji dake yaki da 'yan ta'addan a yankin arewa maso gabas ta 'Operation Lafiya Dole' Kanal Onyeama Nwachukwu shi ne ya bayyanawa manema labarai hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a garin Maiduguri.
Source :naij hausa
Title :
Antura Jiragen Yaki 100 Neman Yan Dapchi
Description : Babban mai baiwa shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari shawara kan harkokin tsaron kasa Manjo Janar Babagana Munguno (Mai Ritaya) a jiya ...
Rating :
5