A ranar Alhamis ne aka gabatar da shugaban kungiyar Jama'atu Ansarul musulimina fi biladil Sudan, wadda ta balle daga kungiyar Boko Haram, wato Khalid al-Barnawi a gaban wata babbar kotun tarayya a birnin Abuja, Najeriya.
Ana dai zarginsa ne tare da wasu mutum bakwai da aikata laifuka da suka shafi ta'addanci, ciki har da sacewa da yin garkuwa da wasu 'yan kasashen waje su 10, da kuma kashe su.
'Yan kasashen wajen sun hada da Turawa da Larabawa wadanda aka sace a jihohin Bauchi da Kebbi da kuma Kano daga 2011 zuwa 2013.
Wadanda ake tuhuma dai sun musanta zarge-zargen yayin da aka dage sauraren karar zuwa watan Afrilu.
A bara ma da aka gurfanar da shi ya yi watsi da tuhumar da ake masa, Sai aka sake yi masa irin tuhumar bayan da wani sabon alkali ya karbi ci gaba da shari'ar.
Ainihin alkalin da ke shari'ar ya fitar da kansa daga shari'ar ne bayan da al-Barnawi ya ce bai yarda da shi ba.
Sojoji ne suka kama Barnawi a shekarar 2016 a jihar kogi da ke tsakiyar Najeriya.
Nigeria: An gurfanar da shugaban kungiyar Ansaru a kotu
An gwabza fada tsakanin 'yan Boko Haram
Amurka ta yi alkawarin bayar da tukwicin dala miliyan biyar ga duk wanda ya taimaka aka kama shi, bayan da suka sanya shi a jerin 'manyan 'yan ta'adda' uku na duniya a sjekarar 2012.
Ansaru wata kungiya ce wadda ta balle daga kungiyar Boko Haram.
Kungiyar na alakanta kanta da kungiyar al-Qaeda.
An daga shari'arsa har zuwa 9 ga watan Afrilu.
Source :bbc hausa
Title :
Ansake Kai Shugaban Ansaru Kotu
Description : A ranar Alhamis ne aka gabatar da shugaban kungiyar Jama'atu Ansarul musulimina fi biladil Sudan, wadda ta balle daga kungiyar Boko Hara...
Rating :
5