A kalla 'yan matan makarantar sakandaren garin Dapchi da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya ne har yanzu ba a ji duriyarsu ba, tun bayan da mayakan Boko Haram suka kai hari garin ranar Litinin da yamma.
Gwamnatin jihar Yoben ce ta tabbatar da rashin sanin inda 'yan matan suke har zuwa wannan lokacin.
Da farko dai an yi tsammanin 'yan matan sun tsere cikin dajin da ke kusa da makarantar ne don su buya, amma har yanzu ba a gansu ba.
Wannan lamari dai ya faru ne shekaru hudu bayan da mayakan kungiyar suka sace fiye da 'yan mata 270 daga makarantar Chibok da ke jihar Borno. wadda ke makwabtaka da Yoben.
Al'amarin da ya jawo hankalin duniya sosai.
Wadanda suka shaida lamarin da ya faru a Dapchin sun ce wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai hari makarantar cikin motoci a kalla 12, suka kuma yi ta harbe-harbe da tayar da ababe masu fashewa, a ranar Lahadi da yamma.
Boko Haram ta kai hari makarantar mata a Yobe
'Satar abinci ce ta kai 'yan Boko Haram makarantar 'yan mata a Yobe'
'Yan BH na jin takaicin ana cewa suna lalata da mu - 'Yar Chibok
Yayin da suka kusanci makarantar, dalibai da malamai sun gudu zuwa cikin daji da ke kewaye wurin, amma har yanzu ba a ga kusan 'yan mata 51 ba.
Mutanen da ke zaune a kusa da makarantar sun shaidawa BBC cewa an gano rabin mutanen da suka bace, wadanda suka buya a kauyuka da ke kewaye da garin.
Amma wasu mazauna kauyukan da ke kewaye da garin sun kira BBC a waya inda suka ce sun ga wucewar mayakan dauke da 'yan mata a motocin nasu.
Sai dai hukumomi ba su tabbatar da cewa ko mayakan Boko Haram din ne suka sace su ba.
Sun kuma ce suna kokarin gano sauran 'yan matan, ta hanyar duba dazuzzukan da ke kewaye da garin.
Wani malami na makarantar, wanda mayakan suka nemi ya ba su hanya su shiga ginin makarantar ya shaida wa BBC cewa mayakan sun je neman abinci ne.
Malamin ya ce ya tabbatar mayakan ba su je makarantar don neman dalibai ba sai don satar abinci da kayayyakin bukatu.
Source:bbc hausa
Title :
Anrasa Yan Mata 51 A Harin Da Boko Haram Suka Kai Makarantar Yobe
Description : A kalla 'yan matan makarantar sakandaren garin Dapchi da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya ne har yanzu ba a ji duriyarsu ba,...
Rating :
5