Rundunar 'yan sanda a Nijeria ta ce ta kama wasu mutane uku da ake zargin suna da hannu a kashe kashen baya baya nan da aka yi a jihar Zamfara.
A cikin wata sanarwa da ke dauke da sa hannun kakakin hukumar 'yan sanda CSP Jimoh Moshood ta ce mutanen na bada hadin kai a bincike da 'yan sanda suke yi.
Ta ce da zarar ta kamala binciken da ta ke yi , za ta gurfanar da mutanen a gaban kotu.
Wadanda ake zargi sun hada Halilu Garba mai shekara 45 da Zubairu Marafa mai shekara 45 da kuma Nafi'u Badamasi mai shekara 40.
Mahara sun kashe sama da mutum '1000 a Zamfara cikin shekara shida'
'Yan bindiga sun kashe akalla mutum 35 a jihar Zamfara
Gwamnan Zamfara 'ya san mutanen da ke kai hari a jiharsa'
Kamen dai na zuwa ne ya yin da 'yan Nigeria ke cigaba da tofa albarkacin bakinsu game da matsalar rashin tsaro a jihar ta Zamfara.
A baya baya nan ne babban supeton yan sanda Ibrahim Idris ya bada umurnin tura da karin da jamian 'yan sanda 130 zuwa jihar ta Zamfara.
Sai dai wasu masana kan harkar tsaro sun nuna shaku kan tasirin da wannan mataki zai wajan dakile ayuikan masu wannan aika aikar.
Source:BBC HAUSA
Title :
Ankama Makasa Uku A Zamfara
Description : Rundunar 'yan sanda a Nijeria ta ce ta kama wasu mutane uku da ake zargin suna da hannu a kashe kashen baya baya nan da aka yi a jihar Z...
Rating :
5