Jami'ai sun ce hari biyu na bama-bamai da aka kai a Mogadishu, babban birnin Somalia sun yi sanadin mutuwar akalla mutum 38.
Hari na farko ya faru ne a kusa da fadar shugaban kasar ranar Juma'a. Na biyu kuma ya faru ne a wani otal da ke kusa da fadar. Mutane da dama ne suka jikkata.
Kungiyar masu tayar da kayar baya ta al-Shabab, wadda ta sha alwashin kawar da gwamnatin kasar, ta ce ita ta kai hare-haren.
An yi ta gumurzu da bindigogi bayan harin da aka kai kusa da fadar shugaban kasar, wanda ya yi sanadin mutuwar masu tayar da kayar baya biyar, in ji jami'ai.
Hare-haren su ne na baya bayan nan da ake dangantawa da kungiyar al-Shabab, wacce ta taba karbe iko da birnin na Mogadishu kafin a kore ta a shekarar 2011 da taimakon dakarun kungiyar tarayyar Afirka.
An kayyade kayan aure a Somalia
'Buhari ne ya jefa Nigeria a yunwa da talauci'
A watan Oktoban da ya gataba, an kashe sama da mutum 500 bayan wani hari da aka kai da motar daukar kaya a birnin. Jami'ai sun dora alhakin kai harin kan al-Shabab sai dai kungiyar
Daya daga cikin hare-haren da aka kai ranar Juma'a ya faru ne bayan wata mota ta ki tsaya a wurin binciken ababen hawa da ke wajen fadar shugaban kasar inda aka tayar da bama-baman da ke cikinta, a cewar kafafen watsa labaran kasar.
Daga nan ne aka soma musayar bude wuta tsakanin masu tayar da kayar bayan da jami'an tsaro.
Daga bisani kuma wata mota da ke ajiye kusa da otal din ta tashi bayan bama-baman da ke cikinta sun tarwatse.
Sai dai al-Shabab ta ce ta hari jami'an tsaro ne.
Ta kara da cewa biyar daga cikin mayakanta, ciki har da direbobi biyu, sun yi shahada sanna ta kashe sojoji 35.
Source :bbc hausa
Title :
Ankai Hari Kusa Da Fadar Shugaban Kasan Somalia
Description : Jami'ai sun ce hari biyu na bama-bamai da aka kai a Mogadishu, babban birnin Somalia sun yi sanadin mutuwar akalla mutum 38. Hari na fa...
Rating :
5